10 Satumba 2025 - 19:23
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hare-Hare A Birnin Sanaa Yamen + Bidiyo

Majiyoyin labarai sun sanar da cewa, an kai hare-hare sama da 6 a birnin Sanaa, babban birnin kasar Yemen.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: A cewar gidan talabijin na Channel 12 na Isra'ila, an kai hare-haren ne kan sansanonin soji, da wurin ajiyar man fetur da kuma wani bangaren yada labarai na Ansarnllah.

Wannan shine bidiyon hare-haren da Isra'ila ta kai kan lardin Al-Jawf da ke arewa maso gabashin kasar Yemen

"Nasreddin Amer" ɗaya daga cikin shugabannin kungiyar Ansarullah ya ce:

Babu wani hare-haren ta'addanci da zai yi tasiri na hana ci gaba da ayyukan sojojin mu na goyon bayan Gaza.

Za mu ci gaba da mayar da martani ga duk wani hari da ake kai wa kasarmu, kuma za mu tsaya tsayin daka wajen tinkarar wannan hare-haren ta'addanci na gwamnati makiya da ke kokarin shafar dukan yankin.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa mutane 9 ne suka yi shahada yayin da wasu 118 suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ta kai a yankin Sanaa da Jawf.

Suma Dakarun Yaman sun tabbatar da cewa: A halin yanzu dai sojojin tsaron saman mu suna fuskantar jiragen yakin Isra'ila da ke Kai hare-hare a kasar mu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha