Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Kamfanin Dryad Global Maritime Security Company: Harin da aka kai kan jirgin Isra'ila Scarlet Ray kusa da gabar tekun Yanbu'a shi ne hari na farko da 'yan Yemen suka kai a arewacin tekun Bahar Maliya.
Wannan ci gaban na nuni da fadadar ayyukan sojojin ruwa na sojojin Yaman a wani yanki da a baya ke da ɗan hadari.
Kenan samun amintacciyar hanya ga jiragen ruwa masu alaƙa da gwamnatocin Isra'ila, Amurka da Birtaniya ya zama kusan ba abu ne mai zai yiwu ba, kuma manyan kamfanoni irin su Maersk da MSC sun canza hanyarsu zuwa Cape of Good Hope; yunƙurin da ya ƙara ƙarin farashin sufuri da inshora.
Your Comment