21 Disamba 2025 - 11:51
Source: ABNA24
Koriya Ta Arewa Ga Japan: Da'awar Tallafawa Zaman Lafiyar Duniya Ba Ta Da Alaƙa Da Kokarin Samar Da Nukiliya

Darektan Cibiyar Nazarin Japan a Ma'aikatar Harkokin Waje ta Jamhuriyar Demokradiyyar Koriya ya bayyana cewa sabuwar gwamnatin Japan tana bin manufofin soja mafi haɗari da tsauri idan aka kwatanta da gwamnatocin da suka gabata.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ya yi gargaɗi game da abin da ya kira "Kwadayin nukiliya na Japan," yana mai tabbatar da cewa neman mallakar  makaman nukiliya na Tokyo ya saba wa ikirarinta na inganta zaman lafiya a duniya. Jami'in ya bayyana cewa ya kamata a yi watsi da waɗannan matakan sosai. Ya ƙara da cewa gyaran da Japan ta yi wa ƙa'idodi uku na adawa da makaman nukiliya da tattaunawarta ta cikin gida game da malakarta makaman nukiliya na barazana ga tsaron yanki da na duniya baki ɗaya.

Bugu da ƙari, darektan Cibiyar Nazarin Japan a Ma'aikatar Harkokin Waje ta Jamhuriyar Demokradiyyar Koriya ya bayyana cewa sabuwar gwamnatin Japan tana bin manufofin soja mafi haɗari da tsauri idan aka kwatanta da gwamnatocin da suka gabata.

Wannan bayanin yana nuna karuwar tashin hankali a Gabashin Asiya, inda batun yaduwar makaman nukiliya ya kasance mafi mahimmanci. Daga mahangar tsaro, a bayyane yake cewa canje-canje a manufofin Japan, gami da sake duba ka'idodinta marasa makaman nukiliya, na iya haifar da:

Ƙarin tashin hankali da amfani da soji a yankin, wanda zai yi tasiri mai yawa ga sauran ƙasashen Asiya da ke neman mallakar makaman nukiliya, da kuma ƙara haɗarin daidaiton diflomasiyya na duniya. A bayyanan ra’ayi saƙon Koriya ta Arewa ba wai kawai gargaɗi ba ne, sai dai tunatarwa ga al'ummomin duniya cewa burin mallakar nukiliya, ko da an gabatar da shi a matsayin mataki zuwa ga zaman lafiya, yana da yuwuwar wargaza yankin da kuma sanya kafa tsaro na gaske a yankin ya zama lamari mai wuya da wahala.

.........

Your Comment

You are replying to: .
captcha