An gudanar da bikin Mauludin Manzon Allah (S) bisa halartar gungun iyalan shahidan kwanaki 12 da sukai shahada a yaki daga sassa daban-daban na kasar Iran, da ma baki daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na duniya baki daya a Husainiyar Imam Khumaini (RA).
Babban birnin kasar Yemen, Sana'a, da sauran lardunan kasar sun gudanar da gagarumin bukukuwa na tarihi na ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal don tunawa da maulidin manzon Allah {SAWA}.