Hizbullah Ta Fara Sake Gina "Rundunar Musamman Ta Ridwan"

Isra'ila Na Yin Matsin Lamba A Siyasance A Labnon
31 Yuli 2025 - 21:15
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Fara Sake Gina "Rundunar Musamman Ta Ridwan"

Rahotanni daga kasar Labanon na nuni da cewa ayyukan tsaro da leken asiri na gwamnatin sahyoniyawa a kan kungiyar Hizbullah ya ci tura, kuma a halin yanzu kungiyar tana kara karfafa tsarinta na gwagwarmaya da kuma fadada matakan dakile wuce gona da iri.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: a yayin da Isra’ila ke amfani da kafar yada labarai da diflomasiyya na kasa da kasa, take yin barazana ga kasar Labanon, ita ma kungiyar Hizbullah tana shirye-shiryen dawo da fagen mayar da martani, ta hanyar gyarawa da kuma karfafa ‘Rundunar Ridwan’. Wannan dai na zuwa ne yayin da matsin lamba na siyasa da diflomasiyya na kasa da kasa musamman Amurka da Faransa ke kara ta'azzara ga gwamnatin Lebanon ta bude dokar takaita mallakar makamai ga gwamnatin kasar ke yi.

Isra'ila na kokarin karfafa yanayin matsin lamba na siyasa a kan Labanon ta kafafen yada labarai da tattaunawa da wakilan kasa da kasa, musamman ta hanyar yin barazanar tsoma bakin soja kai tsaye idan ba a yanke wasu takamaiman qudurori a cikin gida ba. Sabanin yunƙurin diflomasiyya, Isra’ila, yayin da take amfani da kafofin watsa labaru na hukuma, tana aiwatar da manufar ƙara matsin lamba na yau da kullun don shawo kan matakan gwamnati a Lebanon game da barazanar.

An ce Isra'ila, ta hanyar gaggawar gudanar da tarukan cikin gida da kuma gabatar da sakonnin barazanar kai tsaye, tana bin manufar "yin matsin lamba daga waje" domin tunkarar gwamnatin siyasar Lebanon da wani sabon yanayi na gaggawa.

A cikin wannan yanayi, Hizbullah sannu a hankali tana sake gina ikonta na “Rundunar Ridwan” - rukunin manyan dakarunta - ta hanyar daukar dabaru; tsarin da a baya Isra'ila ta yi ikirarin murkushe wani adadi mai yawa na dakarunta da makamanta.

Sabanin haka, an samu daidaito tsakanin gwamnatocin kasashen waje - musamman Amurka da Faransa - cewa dole ne Lebanon ta bude fayil din takaita mallakar makamai a cikin gwamnati da wuri, in ba haka ba, za a aiwatar da tsarin da Isra'ila ta ke riyawa.

A kasar Labanon, abin da ke faruwa a cikin gida shi ne tattaunawa kan kiran wani zama na musamman na gwamnati tare da halartar dukkanin ministocin kasar - da kuma yiwuwar rashin halartar wasu wakilan 'yan Shi'a - tare da sa ran za a yanke shawara kan takaita makamai ga gwamnatin kawai da kuma kayyade lokacin aiwatar da shi.

A sa'i daya kuma, jam'iyyun Lebanon irinsu jam'iyyar gurguzu, da sojojin Lebanon, da jam'iyyar Kataeb, karkashin goyon bayan diflomasiyyar Saudiyya, suna kokarin gabatar da shawarar da za a bi ta hanyar doka ta neman takaita mallakar makamin da ya fi mayar da hankali ga ajandar zaman gwamnati; shawarwarin da kuma wasu jami'an diflomasiyyar Faransa suka goyi bayan.

A wani bangare na wannan tsaka mai wuya, manyan ministocin gwamnatin Lebanon sun jaddada, musamman a tarurruka da wurare na hukuma, cewa idan ba tare da yanke shawara cikin gaggawa kan cikakken ikon takaita mallakar makamai na siyasa da na soja ba, Lebanon na iya fuskantar yanayin da ba a so, inda kai tsaye Isra'ila ta amince da rawar da take takawa wajen tafiyar da harkokin tsaron cikin gidan kasar ko kuma ta kwace shi.

A bangare guda, Isra'ila ta kara matsin lamba na siyasa daga waje a kan Labanon ta kafafen yada labarai da diflomasiyya; A daya bangaren kuwa, dangane da maido da "Ikon Dakarun Ridwan" da Hizbullah ta yi, yana kara matsa lamba a cikin gida. A sa'i daya kuma, Amurka da Faransa, a cikin salon siyasa iri daya, sun yi kira ga Lebanon da ta amince da dokar takaita mallakar makamai sai dai a hannun gwamnati kawai. A cikin kasar Lebanon, ana ci gaba da yunƙurin siyasa da tattaunawa don gudanar da taron gwamnati kan batun takaita mallakar makamai, ko da yake ana tattaunawa kan rikicin cikin gida da rashin halartar wasu ministoci.

...................................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha