Rahotanni daga kasar Labanon na nuni da cewa ayyukan tsaro da leken asiri na gwamnatin sahyoniyawa a kan kungiyar Hizbullah ya ci tura, kuma a halin yanzu kungiyar tana kara karfafa tsarinta na gwagwarmaya da kuma fadada matakan dakile wuce gona da iri.
Sheikh Qassem; ko da duk duniya ta haɗu, ko da kuwa ba ɗaya daga cikin mu da yayi saura. Isra'ila ba za ta iya cin galaba a kan mu ba, har ta kai ga mamaye Lebanon matukar muna raye, muna cewa; "Babu abin bautawa sai Allah".