Yayin da Iran ke jaddada kudurinta na aiwatar da halaltattun haƙƙinta na nukiliya, musamman a fannin inganta makamashin Uranium, matsayar Amurka na ci gaba da yin sirkulle wajen haifar da cece-kuce na siyasa da yiwuwar cimma yarjejeniya.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Wani mai bincike kan huldar kasa da kasa Farshid Bagherian ya shaida wa kafar yada labarai ta Al-Alam cewa: "Na yi imani tun da farko cewa yuwuwar cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka na da yawa, ko da kuwa a matakin da bai dace ba ne. Saboda haka, a cikin wadannan tattaunawa Iran na neman rangwame daga Amurka, kuma Amurka ita na neman rangwame wani abu daga Iran".
Ya kara da cewa, ga Iran, masana'antar nukiliya wani aiki ne na kasa, kuma ba za ta tattauna da kowa ba. Har ila yau, Amurka ba ta da niyyar kai wa Iran hari ta hanyar soji, domin irin wannan harin zai jawo wa Amurka tsada da farashi mai yawa. Amurka ta san cewa idan ba ta cimma matsaya da Iran ba, Iran ma za ta iya yin barazana ga cinikin makamai na Amurka, don haka Amurka ba ta son fuskantar Iran.
Bagherian ya ce: Dangane da kera bam din nukiliya, kuma dole ne in ce muna da fatawa daga Jagoran juyin juya halin Musulunci, wanda a kan haka kera makaman nukiliya haramun ne a shari'ar Musulunci, kuma Amurkawa sun sani sarai cewa wannan fatawar ta wanzu. To sai dai saboda tashin hankalin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta haifar, har yanzu suna cikin damuwa kan Iran ta kera bam din nukiliya, don haka dole ne a kalubalanci gwamnatin sahyoniyawan don kada ta haifar da cece-kuce dangane da hakan.
Your Comment