27 Disamba 2020 - 12:48
Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Haramci Da Amruka Ta Yi Wa Jami’ar al-Mustapha Ta Kasa Da Kasa

A wani bayani da dan majalisa Ruhullah Mutafakkir Azad ya karanta ya bayyana cewa; makiyan ci gaban ilimi sun sake nuna kansu a wannan lokaci, ta hanyar kai farmaki akan cibiya mai girma irin jami’ar Mustafah, wacce tana daya daga cikin muhimman cibiyoyin ilimi na duniya.

ABNA24 : Bayanin ya ci gaba da cewa; Wannan irin matakin yana nuni ne da gajiyawar Amurka da yanke kaunarta akan ci gaban ilimi da al’ummar Iran take yi.

A makon da shude ne dai Baitul-malin Amurka ya sanar da kakaba takunkumi akan jami’ar Mustafa.

342/