18 Nuwamba 2020 - 17:32
Iraki: Mutum Guda Ya Rasu Sanadiyyar Harba Makamai Masu Linzami A Birnin Bagdaza

Majiyoyin labarai na kasar Iraki sun nakalto hukumomin tsaro a birnin Bagdaza babban birnin kasar suna cewa, makamai masu linzami 7 ne suka fadi a tsakiyar birnin a jiya da dare. 4 daga cikinsu sun fada cikin yankin da ake kira “Green Zone “ inda ofishin jakadancin Amurka da wasu kasashen duniya suke ciki.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta da harshen larabci a nan birnin Tehran ya bayyana cewa makaman sun yi sanadiyyar mutuwar wani yaro da kuma jikata wasu 5 a yankinna Green Zone, sannan daya kuma ya fadi kusa da wani asbiti, a yayinda daya kuma ya fadi a cikin lambun Zauraa na Bagdaza sai kuma na karshen ya tarwatse a sama kafin ya iso kasa.

A cikin yan watannin da suka gabata dai, makamai masu linzamu suna ta faduwa a kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagdaza. Sannan a farkon wannan shekarar ne majalisar dokokin kasar ta bukaci dukkan sojojin kasashen waje su bar kasar, musamman sojojin Amurka wadanda suka kashe Janar Shaheed Kasim Sulaimani da abokin tafiyarsa Mahdi Almuhandis.(19)

342/