16 Nuwamba 2020 - 13:37
​An Kawo Karshen Tattaunawar Rikicin Libya Ba Tare Da Kafa Gwamnati Ba

Jakadiyar MDD na musamman dangane da rikicin kasar Libya Stephanie Williams ta bada sanarwan cewa za’a sake bude taron tattaunawa tsakanin yan siyasar kasar Libya a mako mai zuwa bayan da aka cimma yarjejeniyar gudanar da zabe a cikin watan Decemba na shekara mai zuwa wato 2021.

ABNA24 : Williams ta kara da cewa sakamakon taron da ya gabata yana da kyau sosai, don dukkanin mutane 75 da MDD ta zaba don halattan taron sun amince da zabubbuka wadanda za’a gudanar a shekara mai zuwa.

Sannan ta kara da cewa idan sun dawo a makon mai zuwa zasu tattauna kan tsarin da za’a gudanar da zaben na shekara mai zuwa.

MDD ce ta zami mutane 75 daga bangarori daban-daban na kasar don tabbatar da cewa duk mutanen kasr sun sami wakilci a taron.

An gudanar da taron na Tunisia ne bayan da aka dakatar da budewa juna wuta a cikin kasar ta Libya a cikin watan Octoban da ya gabata.(19)

342/