ABNA24 : Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi wa manyan jami’an ma’aikatar shari’a ta kasar ta Iran inda ya ce: Duk da cewa an kori Trump, wanda hannunsa ke jike dumu-dumu da jinin Janar Suleimani, daga fadar White House, Iran ba za ta yi kasa a gwiwa wajen neman a hukunta dukkanin wadanda suke da hannu cikin wannan danyen aiki ba.
Alkalin alkalan na Iran ya ci gaba da cewa ba wai kawai kasar Iran ba ce ta cutu da kisan gillan da aka yi wa Janar Suleimani face dai face dai kasashen musulmi da kuma na yankin nan su ma sun cutu sakamakon tsayin dakan Janar din wajen fada da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda.
A ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne aka kashe Janar Qasim Suleimani tare da mataimakin shugaban rundunar sa kai ta kasar Iraki Abu Mahdi al-Muhandis sakamakon wani hari da sojojin Amurka suka kai musu da wani jirgi mara matuki a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki.
342/