9 Agusta 2016 - 10:31
Karin Tashe Tashen Hankula A Kasar Chadi A Dai Dai Lokacin da Shugaban Kasa Yake Rantsuwar Kama Aiki

An rantsar da shugaban kasar Chadi karo na biyar a matsayin shugaban kasa a jiya litinin a birnin Njamena

A dai dai lokacinda bikin rantsar da shugaban kasar Chadi ya karato an yi ta samun karin tashe tashen hankula na yan adawa a garuruwan kasar da dama. A jiya litinin ne aka rantsar da shugaba Idris Deby a matsayin shugaban kasar ta Chadi karo na biyar. Bakin dai ya sami halattar manya manyan baki daga kasashen waje da kuma cikin gida. Gwamnatin kasar ta Jibge jami'an tsaro a duk manya manyan titunan birnin Njamaine babban birnin kasar da wasu manya manyan garuruwa don hana yan adawa tada hankali.

Jam'iyyun adawar kasar ta Chadi dai suna zargin shugaban kasar Idris Deby da yin magudi da kuma mafani da karfi wajen murkushe yan adawa. Har'ila yau sun zargeshi da amfani da kudaden gwamnati don cimma manufofinsa na mulkin kasar.

A ranar 24 ga watan Afrilu na wannan shekarar ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Chadi inda shugaba Idris Deby da wasu yan takara na jam'iyyun adawa ukku suka shiga takarar neman kujerar shugabancin kasar. Amma sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayar ya nuna cewa shugaban Deby ya lashe zaben tare da samun kashi 66.88% na yawan kuri'un da aka kada. Sai dai hakan bai yawa shuwagabannin jam'iyyun adawar kasar dadi ba, don sun bayyana cewa sakamakon zaben shugaban kasa da ke hannunsu ya nuna cewa ba wanda ya lashe zaben, abinda yakamata hukumar zaben kasar tayi shi ne gudanar da zabe karo na biyu.

Bayan haka ne shuwagabannin jam'iyyun adawar suka kira magoya bayansu da gudanar da ganfami da zanga zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da yadda shugaban Deby yake tafiyar da kasar .

Kafin haka dai jam'iyyun adawar sun kafa wata kungiya ko gamayyar jam'iyyun adawa mai suna FONAC, wacce kuma ta hada jam'iyyun adawa 15 a cikin watan Yuni na wannan shekara. da nufin kalubalantar nasarar da shugaba Idris Deby ya samu a zaben na watan Afrilu. Daga cikin shirye shiryin gamayyar FONAC dai akwai kiran jama'ar kasar su fito kan tutuna don gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewarsu da rantsar da Deby a matsayin shugaban kasa a ranar jiya litinin. A ranar lahadi da ta gabata dai yansanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga zanga. Wasu labarai sun nuna cewa yan sanda sun kashe mutun gida cikin masu zanga zangar a birnin Njamaina. Banda haka jami'an tsaro sun kakkama masu ragin kare hakkin bil'adama da dama kafin a gudanar da bikin rantsarwan na jiya. 

Shugaban Debi dai ya hau kan kujerar shugabancin kasar Chadi a shekara ta 1990 bayan juyin mulkin da yayiwa Hussain Habre, sannan ya sauya kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bashi damar lashe zabubbukan shugaban kasa a shekaru  1996، 2001، 2006  2011 da kuma 2016.