7 Agusta 2016 - 13:54
Jami'an Tsaron Masar Sun Samu Nasarar Halaka 'Yan Ta'adda Da Dama A Yankin Sina Na Kasar

A wani samame da jami'an tsaron Masar suka kaddamar kan maboyar 'yan ta'addan kungiyar Ansar Baiti-Maqdis a garin Arisha da ke Tsibirin Sina na kasar sun samu nasarar halaka gungun 'yan ta'adda ciki har da kwamandansu.

Kakakin rundunar sojin Masar Muhammad Samir a yau Lahadi ya sanar da cewa: Rundunar tsaro ta musamman da ke fada da ayyukan ta'addanci a Masar da taimakon rundunar sojin saman kasar sun kai farmaki kan wata maboyar 'yan ta'addan kungiyar Ansaru Baiti- Maqdis da ke gefen garin Arisha a Tsibirin Sina, inda suka kashe 'yan ta'adda fiye da 45 ciki har da daya daga cikin babban kwamandojin kungiyar mai suna Abu-Du'a Al-Ansari.

Har ila yau sanarwar ta kunshi bayanin tarwatsa wani rumbun makamai mallakin 'yan ta'addan da ya hada da manyan bindigogi da bama-bamai.288