20 Yuli 2016 - 12:11
Sojojin Kasar Faransa Guda Biyu Sun Rasa Rayukansu A Libya

Rahotanni daga kasar Libya sun ce sojojin kasar Faransa biyu sun halaka a kusa da birnin Benghazi da ke gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Sporting ya bayar da rahoton cewa, an harbo wani jirgin yakin kasar Faransa mai safkar angululu a kusa da birnin Benghazi, inda biyu daga cikin sojojin kasar ta Faransa suka mutu, wata kungiyar 'yan tawayen Libya da ke dauke da makamai a Benghazi ta ce ita ce ta kakkabo jirgin.

A kwanakin baya ne Faransa ta aike da dakarunta a asirce zuwa gabashin birnin Benghazi domin taimaka janar Khalifa Haftar wajen yaki da 'yan kungyar ISIS, wadanda suke hankoron kwace iko da birnin na biyu mafi girma a Libya.288