11 Yuni 2016 - 09:30
Dakarun Libya sun kwace tashar jirgin ruwan Garin Syrte

Dakarun Gwamnatin Libya dake samu goyan bayan kasashen Duniya sun kwace tashar jiragen ruwan Garin Syrte daga hannun yan kungiyar Isil.

A can baya dai mayakan IS da ke da’awar Jihadi sun kashe dakarun amintacciyar gwamnatin kasar Libya akalla 32 a ci gaba da fada tsakanin bangarorin biyu a kusa da birnin Sirte.

Karbo tashar ruwan garin Syrte na a matsayin nasara ga kokarin Jinjirar Gwamnatin Lybia na sake tabbatar da cikkaken iko a kasar musaman a wanan gari na Syrte dake a matsayin cibiyar yan kungiyar Isil.288