7 Yuni 2016 - 17:51
Wake da hannu wajen aika-aikar da wasu 'yan daba suka yi yau a Gyallesu?

A yau Talata ne 2 ga watan Ramadan 1437 daidai da 7 ga watan Yuni 2016 wasu 'yan daba da aka bayyana sun zo ne daga wajen unguwar Gyallesu tare da hadin gwiwa da wasu tsiraru 'yan unguwar ta Gyallesu suka rika bin gidajen jama'a da taimakon kayan abinci na watan Azumi ya isa gare su suna fito da shi suna tsiyayarwa.

Akan titi.

Daga jiya da yamma aka fara rabon agajin taimakon kayayyakin abinci na watan Azumi da jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky ya bada umurni a gabatar kamar yadda ya saba a shekarun baya.

Dama a shekarun baya ya kasance yana bada agajin ne ga makwabtan sa na kusa da na nesa.

Su wadan nan 'yan bangar sun rika bi gidajen da aka kai kayan abincin tare da taimakon wasu tsiraru dake unguwar ta Gyallesu wadanda suke nuna musu gidajen, sai su shiga su fito da kayan abincin su fito da shi ko mai gidan ya yarda ko bai yarda ba su farke suna tsiyayarwa.

Daga bisani kuma suka tafi gidan Hajiya Maimuna Yakub kanuwar Sheikh El-Zakzaky wadda take aure a unguwar ta Gyallesu tare da mijinta shekaru masu yawa suka kai mata hari, amma wasu daga cikin jama'ar muhallin suka tare. 

A yayin hada wannan rahoton akwai bayanan dake tabbatar da cewa jami'an tsaro sun zo unguwar don ganewa idan su abin dake faruwa.

Jama'a a ciki da wajen unguwar ta Gyallesu suna ta tofa albarkacin bakin su kan  wannan lamari, suna al'ajabin yadda a irin wannan yanayi da muke ciki da kuma darajar wannan wata na Ramadan wasu zasu dauki nauyin tsare al'ummar musulmi daga alherin da aka yi musu.

Jama'a suna tambaya wadda har yanzun amsar ta ke yawo a zukatan al'umma, suna cewa wa yake yada sharri a unguwar Gyallesu? waye kuma ke yada alheri?

Haka nan kuma har yanzun al'umma ta kasa kunni tana son jin jawabin tambayar ta, cewa wake da hannu wajen ingiza wannan aika-aikar?288