Hoton Bidiyon dai ya kasance na farko da aka nuna ‘Yan matan na Chibok da aka sace a ranar 14 ga watan Afrilu tun wani bidiyo da ya nuna matan suna karatun Al Qur’ani a watan Mayun 2014 wanda kuma ya nuna Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yana ikirarin musuluntar da wasu daga cikinsu tare da aurar da wasu
Wata babban majiyar gwamnati ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa suna nazari akan bidiyon wanda ya nuna ‘Yan mata 15 suna zayyana sunayensu.
Majiyar tace a watan Yulin bara jami’an tsaron Najeriya samu irin bidiyon da kafar CNN ta samu.
Gwamnati ta yi kokarin bin diddigi ba tare da samun nasara ba kuma ‘Yan Boko Haram sun nemi a biya su kudi sama da dala miliyan guda domin sakin ‘Yan Mata 10 a cewar majiyar.
Kafar CNN tace wani mai shiga tsakanin gwamnati da yan Boko Haram ne ya aiko da bidiyon tun a watan Disemba.
Fito da bidiyon dai ya dan sanyaya ran iyayen ‘yan matan na Chibok wanda ke tabbatar da wasunsu suna raye bayan shafe shekaru biyu suna hannun ‘Yan Boko Haram.288