Kamar yadda aka sani ne dai Fulani 'yan bangaren Kautal Ko'e Julbe suna gabatar da bukin maulidin fiyayyen halitta na shekara-shekara a Zariya, a wannan karon saboda halin da ake ciki sun gabatar da bukin ne a garin Gombe tare da kiran a gaggauta sakin Malam.Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288