A wannan ziyara Shugaba Rohani zai ambato batutunwan da suka shafi diflomasiya,kasuwanci da hukumomin kasashen.
Shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran da isa kasar Italiya ya gana a jiya litinin da shugaban kasar Sergio Mattarella kafi daga bisali ya samu ganawa da Firaministan Matteo Renzi.
An cim ma yarjejeniya tsakanin kasashen Iran da Italiya kan batutunwan da suka shafi gayyato mayan kamfanonin kasashen biyu tareda baiwa yan kasuwa damar zuba jari.
Ana sa ran nan gaba Shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya gana da shugaban Faransa Francois Hollande a birni Paris,yayin da masu lura da lamuran siyasar kasar Iran ke kallon ziyarar Shugaba Rohani a matsayi wata nasara a fani diflomasiyar kasar.288