Abdullahyan ya bayyan ahakan ne a daren jiya a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Tehran, inda ya ce tun lokacin da ake gudanar da tattaunawa kan shirin Iran na Nukiliya, masarautar Al Saud ta yi ta kai gwabro ta kai mari domin ganin tattaunawar ta watse, ta hanyar bayar da cin hanci ga wasu kasashe da yi musu alkawulla, amma hakan dai hakan bai yi nasara ba, domin an cimma yarjejeniyar.
Ya ce baya ga hakan ma kuma masarautar ta Al Saud ta tsaya kai da fata domin karya farashin kudin man fetur a kasuwarsa ta duniya domin karya tattalin arzikin Iran, wanda kuma tasirin hakan bai takaita kan Iran ba, ya shafi dukkanin kasashen da suke fitar da danyen man fetur a duniya, wanda kuma ita kanta kasar da ta kitsa wannan kulli lamarin ya fara shafarta kai tsaye.
Ya ce baya ga haka wannan masarauta ta kara kaimi a cikin yan lokutannan wajen taimaka ma 'yan ta'adda da take yi a Syria da Iraki, da kuma kara zafafa hare-hare kan dubban fararen hula da take kashewa a kasar Yemen, baya ga yin sanadiyyar mutuwar dubban alhazai bakin ubangiji da suka tafi safke farali daga dukkanin kasashen musulmi, yanzu kuma ta kashe Sheikh Nimr babban malami a kasar saboda dalilai na siyasa da bangaranci, kuma a sakamakon haka ta yanke huldar jakadancinta da Iran, ya ce yanke alaka da Iran ba zai rufe wadannan munanan laifuka da masarautar taikata ba.288