Carter wanda ke magana a gefen taron ministocin tsaro na kasashen yankin kudanci da gabashin Asiya a birnin Kuala Lumpar, ya ci gaba da cewa jiragen ruwa da kuma na sama musamman ma na yaki mallakar Amurka za su ci gaba da shiga a duk inda suke bukata kamar dai yadda dokokin kasa da kasa suka bayar da damar a yi.
Kafin ikirarin na sakataren tsaro Ashton Carter, akwai wani babban kwamandan sojan ruwan Amurka mai suna Admiral Harry Harris, wanda ya bayyana cewa ruwa da sararin samaniyar duniya mallakar kowa da kowa ne, saboda haka Amurka na da damar shiga a lokacin da ta ga dama.
To saidai ma'aikatar tsaron China ta ce, kasar ta damu a game da kutsen da Amurka ta yi zuwa wannan yankin ruwa wanda yanzu haka China ta gina kananan tsibirrai sama da dubu 12 a cikinsa. 289