30 Oktoba 2015 - 14:37
Taron kawo karshen rikicin Syria

A birnin Vienna na kasar Austria, an bude taron kasashe masu ruwa da tsaki a rikicin Syria, a yunkurin samar da mafita a siyasance ga wannan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar dubbban mutane a cikin shekaru 4.

Taron dai ya hada Ministocin harkokin wajen dukkanin kasashen da ke hannu a wannan rikici, inda a karon farko ministan harkokin wajen Iran ke halartar taron na birnin Vienna, wanda ake kallo a matsayin dama na karshe ga kasashen domin warware rikicin a diflomasiyance.

Ministocin harkokin wajen Rasha, Amurka, Saudiyya, Iran, da kuma Turkiyya duk na halartar wannan taro, kuma kasantuwar wakilan kasashen a wannan tattaunawa, wata alama ce da ke karfafa gwiwa a yunkurin kawo karshen rikicin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane dubu dari uku.

To sai dai majiyoyin diflomasiyyar Amurka na cewa abu ne mai wuya a iya cimma wata matsaya a gaggauce.

Babban magatakarda na MDD Ban Ki-moon wanda ke gudanar da ziyara a birnin Madrid na kasar Spain, ya bukaci kowanne daga cikin bangarorin da ke da hannu a rikici da su yi sassauci domin gaggauta samar da mafita. 289