Nuland ta bayyana haka ne a Kyiv babban birnin kasar Ukraine, a wajen wani taron jami’an siyasa da kuma ‘yan kasuwa na kasashen ketare.
Tace idan aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Minsk baki daya, da ta hada da mutunta diyaucin Ukraine da ya shafi kan iyakarta, daga nan zamu fara janye wadansu takunkumin.
Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suna zargin Moscow da goyon bayan ‘yan ta’awaye masu ra’ayin Rasha da suka shafe watanni goma sha bakwai suna tada kayar baya a gabashin kasar Ukrain, suka kuma kakabawa Rasha takunkumi da dama da nufin
hanata bada tallafin soji da kuma wadansu gudummuwa.