7 Satumba 2015 - 19:04

shugaban hukumar kula makamashin nukiliya ta duniya nukiya Amanu ya bayyana cewa babu kauce hanya game da batun shirin nukiliyar kasar Iran. Amanu ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da hukumar ta gudanar a hedkwatarta, kuma ta bayyana cewa bisa yarjejniyar da aka cimma kasar iran za ta gabatar da cikakken bayani game da halin da shirin nukiliyar kasar yake ciki a da da kuma yanzu domin yin nazari akai,

Shugaban hukumar kula da makamashin Nukiliyar Kasar Iran Yokiya Amanu ya bayana cewa babu kauce hanya ko kadan game da shirin nukiliya kasar Iran na zaman lafiya.

Shugaban na hukumar IAEA ya fadi hakan ne a a wajen taron zango-zango na majalisar da ta gudanar domin bita zaman da majlaisar ta yi tun a watan Agustan da ya gabata , inda yak ara da cewa hukumar ta nukiliya ta duniya ta bas hi damar gudanar da bincike game da batun shirin nukiliyar kasar Iran da ake takaddama akai, bisa jarjejeniyar hadin guiwa da aka cimma tsakanin Iran da kasashen turai 5 gami da kasar Jamus.

Daga karshe shugaban na nukiliya yace sun rattaba hannun da shugaban hukumar nukiliya nakasar Iran Salihi game da batun bada cikakken rahoto kan halin da shirin nukiliyar kasar Iran ya kasace a baya da kuma halin da ake ciki yanzu da hakan zai bawa hukumar damar gudanar da cikakken bincike,kai yadda za su aike da tambayoyin su da mahngarsu akai a 15 ga watan da muke ciki na Satumba288