Daga cikin wadanda suka shiga zanga-zangar dai har da mahaifin Micheal Brown, inda suka yi tattaki har zuwa tsakiyar garin na Ferguson, yayin da aka baza dimbin ‘yan sanda domin tabbatar tsaro.
Masu zanga-zangar dai sun bukaci hukumomi a Amurka da su kawo karshen yadda jami’an tsaro ke kashe jama’a musamman ma bakaken fata a kasar.