Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: Tashar talabijin ta Al-Masirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Amurka sun kai hari a sansanin Sa'ada da ke arewacin kasar Yemen, inda suka kashe mutane da dama a wurin.
Da yawa daga cikin wadanda harin ya rutsa da su fursunoni ne daga cibiyar tsare bakin haure 'yan Afirka da suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a cibiyar gyaran hali da ke birnin Saada bayan da jiragen yakin Amurka suka kai mata hari.
A wani harin kuma Sa'a guda da ta gabata jiragen yakin Amurka sun kai hari a yankin Bart al-Anan da ke lardin Al-Jawf har sau hudu.
Jami’an tsaro na Civil Defence da na Sa’ada na kokarin taimakawa wadanda suka jikkata tare da kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa daga karkashin baraguzan ginin.
Your Comment