27 Afirilu 2025 - 10:27
Source: ABNA24
Yamen Ta Sake Kai Hari Sansanin Navatim Na Isra'ila

Kasar Yemen ta sake kai wani hari da makami mai linzami kan sansanin 'Navatim' na gwamnatin Isra'ila

Kakakin rundunar sojin Yaman ya sanar da cewa, wadannan dakarun sun sake kai hari kan muhimmin sansanin sojin saman Isra'ila na "Navatim" da ke yankunan da aka mamaye da wani harin makami mai linzami.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar sojin Yaman ya sanar da cewa, wadannan dakarun sun sake kai hari kan muhimmin sansanin sojin sama na "Nawatim" na sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke yankunan da suka mamaye da makami mai linzami.

Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Yahya Saree ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Lahadi cewa, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ake zalunta da kuma yin Allah wadai da kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa ke yi wa al'ummar Gaza, bangaren makami mai linzami na sojojin Yaman sun kai hari kan sansanin sojojin sama na "Nawatim" da ke yankin Negev da ke kudancin yankunan da aka mamaye.

Ya ce an gudanar da aikin cikin nasara da wani makami mai linzami da ake kira hypersonic ballistic.

Yahya Saree ya kara da cewa dakarun kasar Yemen za su ci gaba da kara karfin soji da goyon bayan al'ummar Gaza, kuma wadannan hare-hare ba za su tsaya ba har sai yakin Gaza ya tsaya, sannan kuma a kawo karshen killace yankin.

A 'yan sa'o'i da suka gabata, majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa an yi ta karar kararrawa a yankuna daban-daban na yankunan da aka mamaye.

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta kai hari kan wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen kafin ya shiga yankunan da ta mamaye.

Your Comment

You are replying to: .
captcha