Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: Kakakin rundunar sojin Qassam, Abu Ubaida, ya sanar da cewa "mun rasa hanyar tuntuba da gugun jamia’an da ke tsare da sojan Isra’ila Idan Alexander, bayan wani harin bam da Isra’ila ta kai masu kai tsaye".
Kakakin rundunar sojin Qassam, Abu Ubaida, ya tabbatar da cewa, sun rasa hanyar tuntubar gungun dakarunta da suke tsare da sojan Isra’ila Edan Alexander bayan harin bam da Isra'ila ta kai.
A wani sako da ya aike ta kafar sadarwa ta Telegram, Abu Ubaida ya bayyana cewa, "Bisa abunda muke gani shi ne cewa da gangan sojojin mamaya na kokarin share fayil din fursunoni masu dauke da takardar 'yan kasa biyu domin ci gaba da yakin da suke yi na kawar da mutanen mu".
Rundunar Qassam ta fitar da wani faifan bidiyo mai taken "Ku Shirya, Nan ba da dadewa ba 'ya'yanku za su dawo cikin bakaken akwatunan gawa" gawarwakinsu a wargaje da harsashen makamai masu linzami na sojojinku.
Shugabanninku suna son kashe fursunonin kuma dole ne ku shirya wuraren binne su.
Sako daga rundunar Qassam Brigades zuwa ga iyalan fursunonin sahyoniyawan: Majalisar ministocin Netanyahu ta yanke shawarar kashe fursunonin ku, shirya akwatuna da wuraren binne sojojin ku! bidiyon wanda ke nuna yadda jami’an rundunar gwagwarmayar Palasdinawa ke mika gawarwakin fursunonin Isra'ila ga kungiyar agaji ta Red Cross.
Ya kamata a lura da cewa, a cewar takardar da Isra'ila ta gabatar wa masu shiga tsakani kwanan nan, Hamas ta yi niyyar sakin fursuna Alexander Idan a rana ta farko, a matsayin wata alama ta musamman ga Amurka.

Your Comment