Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (ABNA) ya ruwaito, Manjo Janar Mousawi ya ce a wurin bikin tunawa da Manjo Janar Husain Salami: Na yi rashin 'yan uwa masoya. Jarumai, masu sadaukarwa da rashin son kai. Na yi hasarar kwamandoji masu ilimi, haziƙai, masu ƙirƙira da taimako, da sahabbai masu tausayi da gaskiya. Ita ma wannan shahada ta cancanci a taya ta murna. Sun bar iyalansu da jin dadinsu sun shiga fagen fama tsawon shekaru 50 kuma sun ba da rayukansu da tafin hannunsu wajen kare kur’ani da Musulunci da kimar dan Adam mai girma da martabar al’umma da tsaron kasa da kuma abin alfahari ga kasar Iran, tare da sadaukar da duk wani abu da suke da shi.
Manjo Janar Mousawi ya ci gaba da cewa: Na yi aiki da wadannan masoya na tsawon shekaru 30 kuma ina shaida cewa wadannan masoya ba su nemi wani abu domin kansu ba. Shin akwai wani lada da yake jiran wadannan masoya sama da shahada da ladan lahira? Allah ta’ala yayi masu Rahamarsa.
Ya ci gaba da cewa: Babban ɗan'uwana, Laftanar Janar Husain Salami, yana da fitattun halaye. Ya kamata a sanya wadannan halaye a matsayin makaranta ga kwamandoji, manajoji da jami'an kasar. Ya kasance daya daga cikin fitattun kwamandojin tsari kuma kagara wajen kula da Walayatul fikihu. Imani da gaskiya da bin umarnin Jagora ba tare da bindiddiga ko kokwanto ba, rayuwa mai cike da ikhlasi da mahangar tauhidi ga iko da nasara, jajircewa da tsayin daka na babban kwamanda na daga cikin sifofin shahidi Salami.
Ya nanata cewa: Manjo Janar Salami ya yi artabu da makiya ta hanyar fahimtar addini. Yana da ruhin daukaka da samar da fata a cikin al'umma ta hanyar bayyana irin karfin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi. Yana da haduwar imani da ilimi da tawali’u a cikin jagorancinsa. Ya kasance kwamandan juyin juya halin Musulunci kuma abin koyi ga na yanzu da na gaba na sojojin da manajojin kasar.
Manjo Janar Mousawi ya ci gaba da cewa: Tare da hikimar babban kwamandan, jim kadan bayan shahadar Manjo Janar Husain Salami, aka nada Janar na dakarun kare juyin juya halin Musulunci Muhammad Pakpour a matsayin kwamandan wannan cibiya ta juyin juya hali.
Ya yi wa al’umma jawabi da cewa: Ba tare da wuce gona da iri ba, ku al’umma ne abin kauna. Kun tsaya kyam agaban makiya ta hanyar wanzar da hadin kai da hadin gwiwa, kun tilasta makiya durkusawa. Kun bar tarihi mai ɗorewa a jana'izar da girmama shahidan daukaka kuma kun ƙirƙiri sabon almara. Ba zan iya gode muku da wani harshe ba. Kun tabbatar da cewa za mu ci gaba da rike tutar shahidan mu masu girma da daukaka har zuwa digon jini na karshe.
Manjo Janar Mousawi Ya Jaddada Cewa: Fagen Gwagwarmaya Zai Ci Gaba Da Karfafa Da Jinin Wadannan Shahidai.
Yayin da yake jawabi ga makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yi gargadin cewa: Kada makiya su yi farin ciki da daukar rayukan wadannan masoya, muna daukar shahidai a raye a bisa Alkur'ani mai girma. Ya kamata makiya al'ummar Iran su sani cewa al'umma ba su sami daukaka da 'yancinsu cikin sauki ba, sai dai da kishin Qamar Bani Hashim da Imam Husaini da shahidan Ashura. Ba za mu dakata ba har sai mun nunawa wannan tsarin 'yan ta'adda mai kashe yara iyakarsa.
Manjo Janar Mousawi ya jaddada cewa: Makiya sun shirya tsawon shekaru 15 don wannan yakin da suka dora mana. Sun shirya tare da horar da masu kutsawa cikin kasar Iran kuma sun shirya wani tsari da aka lissafa, amma sun yi kuskure a kan abubuwa guda uku: jagoranci, jama'a, da karfin mayar da martani na sojojin kasarmu.
Ya ci gaba da cewa: Batun nukiliya ba wani abu ba ne illa uzirin fakewa na mamaye Iran da rusa gwamnatin cikin mako 48 zuwa guda. Sun yi shirin wargaza kasar Iran, amma al'ummar Iran sun yi nasara. Kamar yadda aka tsara, a mataki na farko, mun ba da martani mai hana ruwa gudu, kuma a mataki na biyu, mun gudanar da wani aiki na ladabtarwa. Sabanin hasashen da suka yi, jama’a sun ajiye matsalolinsu a gefe, suka fito cikin hadin kai da hadin gwiwai. Wadannan su ne dalilan da suka tilastawa Amurka taimakon Netanyahu tare da neman tsagaita wuta domin ceto shi.
Manjo Janar Mousawi ya ci gaba da cewa: Bisa ga umarnin farko na shugabanci, mun tsara wani mummunan shiri, amma bamu samu damar aiwatar da shi ba. Idan har ta sake kai wa Iran hari, to za su ga abin da za mu yi. A wannan yanayin, watakila Amurka ba za ta iya ceto Netanyahu ba. Mu da jama'a a shirye muke.
Your Comment