Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (ABNA) ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran Irna cewa: a yau Asabar sojojin kasar Isra’ila sun yi yunkurin halaka wasu 'yan kungiyar Hizbullah guda hudu a kudancin kasar Lebanon ta hanyar kai wasu hare-hare ta sama da su ka kai.
Majiyar ta yi ikirarin cewa an tabbatar da shahadar dakaran Hizbullah guda daya, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin wasu mutane uku.
A safiyar yau din nan ma gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hari kan wata mota a yankin Bint Jbeil da ke kudancin kasar Labanon
Dangane da haka ne cibiyar bayar da agajin gaggawa ta likitoci da ke da alaka da ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu biyu kuma suka jikkata sakamakon harin da jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan suka kai kan wata mota a yankin "Saf al-Hawa" da ke Bint Jbeil a kudancin kasar.
A baya makiya yahudawan sahyoniya sun kai hari a yankuna da dama a kudancin kasar Lebanon a wasu hare-hare a jiya Alhamis.
Keta iyakar yarjejeniya a kullun na cin gashin kan kasar Labanon da kuduri mai lamba 1701 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Sahayoniya ta ke yi ya haifar da tambayoyi masu tsanani game da tattaunawar da suke ke riyawa da ta dogaro kan diflomasiyya don kare kasar Labanon daga zaluncin sahyoniyawa.
A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin saman Isra'ila ta yi ikirarin kai hari kan sansanonin sojin Hizbullah da ma'ajiyar kayan aikin soji a kudancin Lebanon.
A cewar wani rahoto da kafar yada labaran Isra'ila ta "E24" ta fitar, sojojin gwamnatin kasar sun yi ikirarin cewa, sojojin saman kasar karkashin jagorancin hukumar leken asiri da na arewacin kasar sun kai farmaki kan wuraren da sojojin da suka hada da ma'ajiyar kayan yaki na Hizbullah, gine-ginen soji, da ababen more rayuwa a kudancin kasar Lebanon.
Tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra'ila sun keta wanna yarjejeniya sau da dama, lamarin da ya kai ga shahada da jikkata wasu 'yan kasar.
Tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Isra'ila da Lebanon tare da shiga tsakani na kasa da kasa ta fara aiki da safiyar yau Laraba 27 ga watan November 2024.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana a daren Larabar da ta wuce cewa: tun bayan da aka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta kusan sau 3,700.
Your Comment