4 Yuli 2025 - 19:04
Source: ABNA24
Masoya Da Makiya Imam Husaini (AS) A Mizanin Darasin Tarihi

Me ya sa za dole mu san masu kyawawan ayyuka da marassa kyau? Ta yaya za mu koyi darussa na rayuwa daga gare su? Gabatar da sahabban Imam Husaini (AS) da wadanda suka kafa tarihi a Karbala shi ne haske mai shiryarwa a gare mu a yau. A daya bangaren kuma, darussa masu daci na rayuwar Yazid da sahabban Umar Sa’ad suna tunatar da mu nutsuwar mutum a tafarkin bata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (AS) na kasa da kasa, Abna - Tarihi madubi ne na bil'adama wanda a cikinsa ake nuna munana da kyawawan ayyuka a bangarori da ke fuskantar juna. A halin yanzu, sanin masui kyawawan ayyuka da masu munanansa ba wai kawai yana shiryar da mu zuwa ga hanya madaidaiciya ba ne, a’a, muna koyon darasi daga kura-kurai da zamewa na magabata. Rayuwar sahabban Imam Husaini (AS) irin su Zuhair bin Qain da Habib bin Mazahir cike suke da darussa na imani da sadaukarwa. Sabanin haka, Yazid da Umar Saad sune a misalan nutsewar mutum a cikin ɓangarorin ɓarna da ka iya zama gargaɗi a gare mu.

Mazaje Nagartattun Tarihi Sune Fitilar Jagoran Dan Adam

Nagartattun mutanen tarihi kamar taurari ne masu haskaka hanyar rayuwa. Sahabban Imam Husaini (AS) misali ne na wadannan fitattun mutane da suka tashi tsaye wajen kare gaskiya da sadaukarwa ta hanyar sadaukar da rayukansu da dukiyoyinsu. Zuhair bin Qain yana daya daga cikin wadannan sahabbai masu aminci wadanda suna sane bisa zabin kansu suka zabi su goyi bayan Imam Husaini (AS). Shi ya kasance wanda a da mai goyon bayan Uthman, ya canza salon rayuwarsa bayan ya ji maganar Imam Husaini (AS) kuma ya zama daya daga cikin makusantansa  masu taimaka masa(1).

Haka nan Habib bin Muzahir shima wani fitaccen sahabin Imam Husaini (AS) ne wanda aka san shi da kaunarsa da amincinsa ga Ahlul Baiti (AS). Shi ya kasance daya daga cikin manya-manyan mutanen Kufa, ya garzaya don taimakon Imam da dukkan karfinsa, har ma ya sadaukar da rayuwarsa a kan haka (2). Wadannan mutane abin koyi ne a gare mu ba kawai a fagen fama na Karbala ba, har ma a kowane lokaci na rayuwarsu.

Har a yau, ta hanyar karanatwa da yin nazarin rayuwar waɗannan manyan mutane, za mu iya koyan darussa masu girma na jarumta, bangaskiya, da sadaukarwa. Sun nuna yadda ake tsayawa tsayin daka wajen yaki da zalunci da taimakon gaskiya.

Lalatattun Mutane A Tarihi Sun Kasance Darussa Daga Zamewar Bil'adama

Sabanin masu kyawawan ayyuka, akwai wasu a tarihi da suka zama misali na faduwar bil'adama. Yazid ibn Muawiyah yana daya daga cikin bakar fuska a tarihin Musulunci, wanda da dabi'unsa marasa dadi, ya nuna yadda mutum zai kauce daga tafarkin gaskiya. Ya tashi da tarbiyar Banu Umayya, wanda ya bar bakin tabo a tarihin Musulunci ta hnayar yin zalunci da keta da wuce gona da iri (3).

Sahabban Umar Sa’ad su ma sauran misalai ne na bata da karkacewa da baudewa. Umar Sa’d wanda da farko ya yi niyyar komawa Kufa da gujewa fada da Imam Husaini (a.s.), daga karshe ya mika wuya ga kwadayin duniya da alkawarin Yazid ya bata hannunsa da jinin dan Manzon Allah (s.a.w.) (4). Waɗannan mutane darussan gargaɗi ne mai tsanani a gare mu game da yadda son duniya da sakaci ke kai mutum ga halaka.

Sanin waɗannan munanan fuskoki yana taimaka mana mu zaɓi tafarkin rayuwarmu da kyau kuma mu koyi daga darussan da kurakuransu ke nunawa.

Darasi Da Zamu Dauka A Yau; Tarbiyantarwa Da Ilimantarwa Ga Tsatso Mai Zuwa Nan Gaba

Daya daga cikin muhimman sakonnin da za a iya koya daga rayuwar nagartattun mutane da lalatattun mutane, shi ne muhimmancin ilmantar da al’umma masu zuwa. Yazid ibn Muawiyah misali ne na tarbiyar da ba daidai ba, wanda ya haifar da zalunci da zaluncin Ahlul Baiti (a.s). Sabanin haka, Zuhair ibn Qain da Habib ibn Muzahir sun kasance samfurori na ingantaccen tarbiya, waɗanda suka iya yanke shawara mafi kyau a lokuta masu mahimmanci a tarihi.

A yau kuma ya zama wajibi a garemu mu ilmantar da al’umman da za su zo nan gaba bisa koyarwar Ahlul Baiti (a.s) ta yadda za su iya jure wa kalubalen rayuwa. Ilimantarwa da tarbiyar da suka ginu a kan imani da kyawawan halaye da sanin ya kamata na iya haifar da zuriya kamar sahabban Imam Husaini (a.s) su zama hasken shiryar da al’umma.

Tarihin Musulunci yana cike da fitattun mutane da za su iya zama abin koyi a gare mu, walau a kan tafarkin gaskiya ko na bata. Sanin nagartar irin su Zuhair bn Qayn da Habib bn Muzahir yana shiryar da mu zuwa ga haske. A daya bangaren kuma, daukar darasi daga miyagun mutane kamar Yazid da Umar Saad gargadi ne da a guji bata. A yau ya zama wajibi a gare mu mu zabi hanya madaidaiciya ta hanyar nazarin wadannan fuskoki da kuma ilimantar da al’umma masu zuwa ta hanya mafi kyawu.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------

Madogara:

1. Sheikh Mufid, Al-Irshad fi Ma’rifat Hujajillah Ali Al-Ibad, juzu’i. 2, ku. 91.

2. Ibn Shahr Ashhub, Manaqib Al A’li Abi Talib, juzu’i. 4, ku. 107.

3. Tabari, Tarikh Umma Wal Maluk, vol. 4, ku. 313.

4. Allama Majlisi, Bihar al-Anwar, vol. 45, ku. 66.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha