A'shura-Tanzaniya

Ilimantarwa Akan Waki'ar A'shura Da Duk Wani Lamari Na Tarihin Musulunci Shi Ne Kiyaye Gaskiya Da Adalci A Tarihi.

Ilimantarwa Akan Waki'ar A'shura Da Duk Wani Lamari Na Tarihin Musulunci Shi Ne Kiyaye Gaskiya Da Adalci A Tarihi.
6 Yuli 2025 - 19:28
Source: ABNA24
Ilimantarwa Akan Waki'ar A'shura Da Duk Wani Lamari Na Tarihin Musulunci Shi Ne Kiyaye Gaskiya Da Adalci A Tarihi.

Muna karanta abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci domin mu ilmanta daga garesu bayan mun karantu da ilmantu sai mu yi dogaro da Adalci mu Fadi Gaskiyar Tarihi kamar yadda aka rubuta a Ingantattun Madogaran Shi'a da Sunna.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (A.S.) -- ABNA – ya habarta cewa: an gudanar da makokin Ashura a kasar Tanzaniya cikin nasara a wannan shekara ta shekara ta 1447 bayan hijira. Shugabanni daban-daban na cibiyoyin Musulunci da na Gwamnati sun halarci wannan Muzahara ta lumana da aka gudanar a rukunin gidan waya da ke Dar-es-salaam - Tanzania. Wadannan shugabannin sun hada da Hujjatul-Islam Wal-Muslimin, Dr. Ali Taqawi - Shugaban Jami'at Al-Mustafa (s), Tanzania. Sauran sun hada da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar Tanzaniya, Musa Azan Zungu da sauran shugabannin gwamnati da malamai.

Bayan zaman makoki a cikin zauren Hussainiyya, a ranar goma ga watan Muharram, an gudanar da tattaki akan hanyoyi uku daban-daban. Mabiya da Masoya Ahlul-baiti (as) a duk fadin duniya, a yau sun fito sun gudanar da tattaki a kan tituna tare da daga murya a cikin sautin juyayin kisan gillar da aka yi wa Jikan Manzon Allah (saww) a Karbala.

A Tarihi: A shekara ta 61 bayan hijira, wani lamari ya faru wanda littattafan tarihi suka ruwaito, shi ne kisan gilla da aka yi wa jikan Manzon Allah (saww), Al-Imam Al-Husin (a.s) da Sahabbansa.

Ba wai mugayen azzaluman sun kashe shi da zalunci ba ne domin yana da laifi, babu shakka! Badon haka ba ne ba shi da wani laifi, sai don kawai ya ki bai'a ga fajiri, wanda ya dora kansa a matsayin mai mulkar al'ummar musulmi, wanda ya shahara da kazantar shaye-shaye, da wasa da mata a bainar jama'a, da kisan kai, da munanan halaye, kuma ba kowa ba ne face fasikin Yazidu bin Mu'awiya (L.A).

Masana tarihi sun rubuta wannan da ma fiye da haka don mutane su karanta su waye, su san Gaskiya da Karya su nesantar da kansu daga karya.

Idan ka ga musulmi suna zaune suna Magana kan waki'ar Ashura suna yin Allah wadai da kisan gillar da Yazid bin Mu'awiya yayiwa Imam Husain As da sahabbansa....ka sani cewa to sun anbaci dukkan abubuwan da suka faru na tarihi da suke cikin littafan Sunna da Shi'a game da waki'ar Karbala... kuma sun karanta ne sannan suka waye, yanzu kuma sun tsaya a kan gaskiya game da sahihin tarihin d aka rubuta akan Waki’ar Karbala da Ashura da ma hatta yunkurin musulunci na Imam Husaini (a.s).

Your Comment

You are replying to: .
captcha