Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) ya kawo cewa, an gudanar da taron majalissar Tasu’a a Kwalejin Al-Mustafa (s) - Malawi domin tunawa da shahadar Imam Husaini (as). Wanda ya gabatar da wannan majalisi shine: Sheikh Talib Khamis Maduka. Kuma batun da aka tattauna shi ne: "Dalilin da ya sa Imam Husaini (a.s) ya ki goyon bayan Yazid".
A cikin jawabinsa a ranar Tasu’a (rana ta tara ga Muharram), Sheikh Talib Khamis Maduka ya bayyana babban dalilin da ya sa Imam Husaini (a.s) bai taba yarda da bai’a ga Yazid (la).
Imam Husaini (a.s) ya sani cewa Yazid bin Mu’awiya fajiri ne, wanda ya ke da munanan halayya kamar:
1_Kasancewar mashayin giya.
2_ Dan wasan caca.
3_ Haka zalika yayi luwadi.
4_ Yayi kwarkwasa da mata a bainar jama'a.
5_ Ya aikata zunubai a fili da rashin kunya.
Bayan kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (a.s) mabiya Yazid sun gudanar da gagarumin biki inda suka sha barasa da yawa a matsayin nuna murnar kisan gillar da aka yi wa jikan Annabi Muhammad (s.a.w.w).
Imam Husaini (a.s) bai yarda ya mika wuya a gaban irin wannan fajiri ba, domin Musulunci ba zai taba kasancewa a karkashin wani fajiri kuma gurbataccen shugaba kamar Yazid bin Muawiya (la) ba.
Wannan wa'azin wani bangare ne na bayanin da aka gabatar a taron Tasu'a wanda reshen Jami'atu Al-Mustafa (s.a.w.w) na kasar Malawi suka shirya.













Your Comment