6 Yuli 2025 - 15:28
Source: ABNA24
Miliyoyin Mutane Ne Suka Gudanar Da Tarukan Ashurar Imam Husaini As A Beirut

An gudanar da tattakin Ashura a yankunan kudancin birnin Beirut tare da halartar iyalan shahidai da waɗanda aka raunata masu gwagwarmaya da kuma bangarori daban-daban na al'ummar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau Lahadi dubban mutane ne suka hallara a yankin kudancin birnin Beirut domin gudanar da tarukan tunawa da ranar shahadar Imam Husaini bn Ali (AS) da sahabbansa a Karbala.

Duk da cewa Sayyid Hasan Nasrallah bai halarci wannan taro na bana ba a bayyane da gangar jikinsa ba, amma ruhinsa da ruhiyyarsa sun kasance a cikin zukatan jama'ar da suka halarci taron, kuma wadanda suka halarci taron suna rera takensa da ya saba yi, musamman ma kalmar "Inna Alal-Ahd ya Nasrallah" (Muna kan alkawari ya Nasrallah).

Hotunan shahidan Sayyid Hasan Nasrallah sun bayyana a sassa daban-daban na wannan tattakin, kuma fuskarsa na dauke da tutoci kanana da manya, har ma ana iya ganin fuskarsa a baranda da tituna, lamarin da ke nuni da irin matsayinsa na ruhi da jagoranci a tsakanin al'umma.

Baya ga hotunan Sayyid Nasrallah, mahalarta taron sun kuma rike tutocin Imam Husaini (AS) don nuna alakar da ke tsakanin tafarkin Karbala da tafarkin gwagwarmaya.

An gudanar da tattakin ne tare da halartar bangarori daban-daban na Ahlus-Sunnah da iyalansu, da kuma masu raunuka na gwagwarmaya da iyalan shahidai sun kasance a sahun gaba.

An fara wannan gagarumin taron ne bayan kammala taron koli na kungiyar Hizbullah a cibiyar Sayyudush Shuhada da ke kudancin birnin Beirut a safiyar yau, kuma masu tattakin sun amsa kiran Imam Husaini (AS) tare da rera taken "Ba Za mu Barka Ka Ya Hasan, ba za mu taba karbar wulakanci ba."

Ya kamata a lura da cewa a yau ne 10 ga watan Muharram miliyoyin al'ummar musulmi a duniya ke gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Husaini (AS).

Your Comment

You are replying to: .
captcha