6 Yuli 2025 - 22:24
Source: ABNA24
Sheikh Ibrahim Alzakzaky {H}: Mutum Ya Tsaya Ƙyam Tsakani Da Allah, Ƙyam Saboda Allah, Ko Me Zai Faru Ya Faru.

Jagora ya gana da ba'adin 'yan uwa a Asabar 9 ga Almuharram 1447 a gidansa da ke Abuja, a munasabar juyayin Shahadar Abi Abdullahil Husain (AS).

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya bayar da rahoton cewa: A yayin jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana Ashura a matsayin alama da ta fita daban, inda yace, babu yini kamar ranar Ashura, domin yini ne da ya alamta dukkannin zalunci. “Duk irin wani zalunci da za ka siffata ya auku a doron duniya to Ashura ya alamta shi. Don haka Ashura darasi ne babban gaske, shi yasa raya shi raya addini ne.”

Yace, Imam Husaini (AS) ya fito ne da nufin kawo gyara a al'ummar kakansa (S), da yin umurni da kyakkyawa da hana munkari. “Wannan sai ya ƙare a bayar da kansa (a yanka) a Karbala. To wannan abinda ya fito dominsa, wanda shi ne ya karata da yin Shahada, shi ne muke rayawa. An ce masa ko dai ya mika wuya ne a fasa wannan, ko kuma (ya miƙa) kansa, sai ya ba da kansa. Don haka muke cewa, shi Imam Husaini (AS) ya yi 'thaura', wato ya yi juyin-juya-hali, ya sauya tunanin mutane, ya nuna musu cewa, ba a karɓan zalunci, ba a yarda da zalunci, ba a bin azzalumai.”

Jagora ya bayyana nasara a matsayin tsayawa ƙyam a tafarkin Allah ko da za a Shahadantar da mutum kamar yadda Imam Husaini (AS) ya yi. “A wasikar Imam Husaini (AS) ga yan uwansa, ya ce musu, wanda ya biyo ni zai yi Shahada, kuma wanda ya zauna ba zai yi nasara ba. To ku fada mini, mece ce nasara? Shahada.”

Yace, “Da ace Imam Husaini ya miƙa wuya ne, sai ya zauna lafiya ya yi wa'azi, ka ga kenan da yanzu ya zama Sunnah, in ka tashi kace ya kamata a kawo sauyi, sai a ce ka kai Imam Husaini ne, da ya ga abinda ya gani ai miƙa wuya ya yi, saboda haka don me kai ma ba za ka miƙa wuya ba? Da sai miƙa wuya ga azzalumai ya zama shi ne addini.

Jagora ya bayyana cewa, har yanzu mutum na da damar kasancewa tare da Imam Husaini (AS) kuma ya samu rabo irin na wanda suka kasance tare da shi. “Duk wanda kuka gan shi yanzu yana mara ma azzalumai baya, in a wancan lokacin yake, wa zai mara ma? Azzalumai. Wanda ka ga ya dake akan sai dai ko a kashe shi, amma ba zai bar tafarkin Allah ba, to irin shi ne zai bi Imam Husaini da ace ya zo a lokacinsa."

Yace, inda za ka tambayi Namarud wa kake so ka kashe? Zai ce Ibraheem (AS). Firauna kuma wa yake so ya kashe? Musa (AS). Lokacin Manzon Rahma (S) su Abujahal, Walid Bin Mugira, Abu Sufyan bin Harb duk wa suke son su kashe? Annabi (S). A lokacin Mu'awiyya Dan Abisufyan, lokacin Ali (AS) na raye, inda za ka tambaye shi wa yake so ya kashe? Zai ce Amirulmuminin (AS). To Yazidu kuma wa yake so ya kashe? Imam Husaini (AS). To yanzu fa, Trump da Netanyahu wa suke so su kashe? Sayyid Khamenie. Don haka yace: “Ka ga kowane Fir'auna da Musansa. Ya kamata ka san wane ne Fir'aunan wannan zamanin, wane ne kuma Musa a wannan zamanin. In ka san wannan za ka gane wane ne Yazidun zamaninka, wane ne Husainin zamaninka... Saboda idan kana tare da Yazidun yau, ba abinda zai raba ka da Yazidun zamanin jiya in da a zamanin ka zo.”

A karshe, Jagora (H) ya yi kira da mu ɗauki darasin da Ashura ke koyar da mu na sadaukarwa da tsayawa ƙyam ba tare da wasu dabaru ba. “Mutum ya tsaya ƙyam tsakani da Allah, ƙyam-ƙyam-ƙyam saboda Allah, ko me zai faru ya faru. Sadaukarwa saboda Allah, saboda Allah, saboda Allah. Mu ɗauka ma kawukanmu wani alƙawari guda; mu ɗauka ma Imam Husaini (AS) alkawarin cewa abin nan da ya fito dominsa, za mu cigaba daga inda ya tsaya har ya zuwa bayyanar wanda da bayyanarsa ne za a samu mafita insha Allah, Allah Ya gaggauta bayyanarsa.”

Daga Sayyid Ibraheem Zakzaky Office (H) 

Ashura1447 

09/Al-Muharram/1447

05/July/2025

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha