6 Yuli 2025 - 14:49
Source: ABNA24
Miliyoyin Masoya Imam Husaini Ne As Sun Halarci Karbala Duk Da Tsananin Zafi

Miliyoyin mabiya da masoya Imam Husaini As ne suka hallara a Karbala duk da zafin rana

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya kawo rahoton cewa: Miliyoyin maziyarta daga sassa daban-daban na duniya ne suka gudanar da taron juyayin Ashura na shahadar Imam Husaini a hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma Sayyidina Abbas (AS).

 Miliyoyin maziyarta daga kasashe daban-daban ne suka hallara a Karbala a yau, 10 ga watan Muharram, domin tunawa da ranar Ashura ta Husaini a hubbaren Imam Hussain (AS) da dan uwansa Sayyid Abul Fadl Abbas (AS).

Wuraren biyu masu tsarki sun cika makil da mabiyan Imam Hussaini (AS), wadanda duk da tsananin zafin da ake ciki, sun nuna sha’awarsu da shauƙinsu na nuna alhini da jajanta wa iyalan gidan manzon Allah tare da yin musharaka cikin bakin ciki na wannan musiba.

Har ila yau shugabannin Haramin Imam Husaini sun aiwatar da wani tsari na tsaro da tsari na tabbatar da zaman lafiya a ranar Ashura, wanda ya hada da tura jami'an tsaro na musamman a ciki da wajen hubbaren, da harba na'urorin gano bama-bamai, da kuma ci gaba da hada kai da jami'an tsaro da kuma hukumar gudanarwar Karbala. An kuma baza tawagogin ceto da kashe gobara a muhimman wurare hudu domin samar da ayyukan da suka dace ga maziyartan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha