11 Maris 2025 - 09:35
Source: ABNA24
Iran Da Rasha Sun Fara Aikin Hadin Gwiwa Don Gano Sinadarin Lithium Na Iran

Kasashen Iran da Rasha sun fara hadin gwiwa don gano albarkatun lithium a Iran. Ya zuwa yanzu, an gano adadin wannan karafa a cikin lardunan Qum, Isfahan, da Semnan. Kwararru na Rasha da manyan dakunan gwaje-gwaje na kasar su ma sun shiga cikin wadannan binciken.

A baya jaridar Sahayoniyya Ma'ariv ta bayar da rahoton cewa, gano sinadarin lithium a Iran zai iya canza ma'auni na makamashi. Binciken farko ya nuna cewa akwai wasu adadin lithium a cikin waɗannan fagagen, amma darajar tattalin arzikin sa ya fi matakin da aka gano. Lithium, karfe mafi sauƙi a duniya, yana taka muhimmiyar rawa a masana'antar baturi da makomar makamashi a duniya.

Saleh Ghasemi kwararre a fannin hakar ma'adinai ya tabbatar da cewa, adadin lithium na Iran ba shi da wani muhimmanci, don haka ya kamata a mai da hankali kan hakar sinadaran karafa kamar karfe da tagulla. Amma Abbas Rahmani, wani masani, ya ce: "Yankin Iran yana da girma sosai, kuma muna da albarkatun lithium masu yawa wadanda har yanzu ba a gano su ba". "Fatan gano lithium a kasar yana da yawa gay an kasar".

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha