27 Disamba 2025 - 20:32
Source: ABNA24
Yadda Amurka Ke Hana Ƙasashen Larabawa Koyar Da Haƙiƙanin Alkur'ani

Labarin wani Farfesa ɗan ƙasar Kuwait game da matsin lambar da Amurka ke yi wa ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Farisa

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Dr. Abdullah Al-Nafisi, farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Kuwait, ya yi nuni da matsin lamba kai tsaye daga Washington a cikin wani rahoto game da tsoma bakin Amurka a harkokin ilimi na ƙasashen Larabawa na Tekun Farisa.

A cewar Al-Nafisi, Liz Cheney, 'yar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka Dick Cheney, a lokacin da ta kai ziyara Kuwait, ta yi kira da a cire wasu ayoyi daga Alƙur'ani Mai Tsarki da suke magana akan Yahudawa daga cikin manhajar ilimin makarantun ƙasar, sannan ta jaddada cewa ya kamata a gyara manhajojin karatun bisa ƙa'idodin da Amurka ke so.

Waɗannan kalamai suna nuna suka ga tsoma bakin siyasa da al'adu na Amurka a cikin tsarin ilimi da asalin ƙasashen yankin.

Menene haɗin kasashen larabawa da tsarin Amurka ko wace kasa da tsarin ta akwai dokar da ta ke bi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha