Mujallar Newsweek ta tattauna batun fara atisayen da aka yi tsakanin Iran da Rasha a tekun Kaspian a wata makala, inda ta bayyana shi a matsayin sako ga Amurka game da hadin gwiwar Tehran da Moscow.
Kasashen Iran da Rasha sun fara hadin gwiwa don gano albarkatun lithium a Iran. Ya zuwa yanzu, an gano adadin wannan karafa a cikin lardunan Qum, Isfahan, da Semnan. Kwararru na Rasha da manyan dakunan gwaje-gwaje na kasar su ma sun shiga cikin wadannan binciken.