3 Maris 2025 - 21:38
Limamin Juma'a Na Bagadaza Ya Tabbatar Da Ci Gaba Da Yi Gwagwarmaya Da Isra'ila

Sayyid Yassin AlMusawi: Jana'izar da aka yi a birnin Beirut ga jagoran gwagwarmaya Sayyid Hassan Nasrallah, wani muhimmin al'amari ne da ke nuna matsayin mutumin da kuma rawar da ya taka a fagen gwagwarmaya da Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As ABNA ya habarto maku cewa, a cikin hudubar Juma’a da Ayatullah Sayyid Yassin Musawi, Limamin Juma’a na Bagadaza ya gabatar, yayi nazari kan fitattun abubuwan da suka faru a makon da ya gabata, wadanda ya bayyana su a matsayin “Muhimman al’amura da ke bukatar bada lokaci domin tunani da nazari akansu”.

A cikin jawabin nasa, Sayyid AlMusawi ya yi ishara da gagarumin taron jana'izar jagoran gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon shahidi Sayyid Hassan Nasrallah, inda ya bayyana shi a matsayin shahidin al'umma.

Ya bayyana cewa jana'izar da aka yi a birnin Beirut ga jagoran gwagwarmaya Sayyid Hasan Nasrallah, wani muhimmin al'amari ne da ke nuna matsayin mutumin da kuma rawar da ya taka wajen jagorantar gwagwarmaya da Isra'ila.

Ya jaddada cewa, Sayyid Nasrallah ya jagoranci wata fafutukar gwagwarmaya da ta hada da Falasdinu, Labanon, Siriya, Iraki, Yemen, har ma da sauran yankuna. Ya kara da cewa, wannan tsayin daka ya iya haifar da wani sabon lamari a yankin, duk kuwa da irin bambancin kayan aiki da kayan tanadi da ke tsakanin dakarun Isra'ila da na Amurka.

Ayatullah Musawi ya ce: Yakin ba wai yaki ne na makamai ko kayan aiki ba, a'a yaki ne na karfin azama da imani, Shahid Nasrallah ya kasance yana sane da cewa babu daidaito tsakaninmu da Amurka da Isra'ila a makami ko fasaha, amma ya tabbatar da hakan da imani na iya samun nasara.

Fitaccen malamin nan na makarantar hauza a Najaf ya jaddada cewa, duk da shahadar Sayyid Nasrallah, yakin da ake yi da Isra'ila bai kare ba, kuma har yanzu al'ummar kasar na iya fuskantar kalubale. Ya yi nuni da cewa gagarumin taron jana'izar da garuruwan larabawa da dama suka halarta, da suka hada da Najaf da Basra na kasar Iraki, da Iran, Yemen da Bahrain, wani sako ne karara cewa ruhin gwagwarmaya na nan daram.

Jagoran ya kara da cewa: Har yanzu al'ummar da ta haifi shugaba irin Sayyid Nasrallah al'umma ce da ke ci gaba da haihuwa, wanda suke da ikon yin abun ake ganin bazai iya faruwa ba, kuma gagarumin taron jana'izar da aka yi a kasar Labanon da sauran garuruwan Larabawa ya tabbatar da cewa mu al'umma ne masu gwagwarmaya, kuma ba za mu yi watsi da hakkinmu ba.

Limamin Juma’ar Baghdad ya kuma yi tsokaci kan batun kulla alaka da Isra'ila, yana mai la'akari da hakan a matsayin babban kalubale ga al'ummar Larabawa. Ya yi nuni da cewa, akwai ‘yan tsiraru da ke kira da a daidaita da su bisa hujjar samun daidaiton tattalin arziki, yayin da mafi yawansu suka ki amincewa da wannan matakin, suna la’akari da hakan na nufin mika wuya ga aikin Isra’ila.

Ya ce: "Akwai masu son daidaita alakarsu da Isra'ila bisa zargin samun saukin tattalin arziki, amma muna tabbatar da cewa daidaitawa ba zai samu zaman lafiya ba, sai dai zai kara karfafa ikon da yahudawan sahyoniyawan suke da shi kan yankin. Kasashen Larabawa da na Musulunci ba za su amince da mika wuya ba".

Jagoran ya yi ishara da matsayin gwamnatin Al-Julani a kasar Siriya da kuma ayyana mika wuya ga sahyoniyawa yana mai cewa: Shin sahyoniyawan sun gamsu da jawaban Al-Julani na daidaitawar kuwa? Ko shakka babu, yahudawan sahyoniya sun yi ruwan bama-bamai kan dukkanin karfin sojan kasar Siriya tare da mamaye yankuna da dama na kasar Siriya, yayin da al-Julani ya shagaltu da kashe shugabanni da hafsoshin sojojin kasar ta Siriya.

Ya yi jawabi ga masu kira da a daidaita alaka da sahyoniyawa da cewa su masu laifi ne, yana mai cewa: Ku dubi Al-Julani da Sham da abin da hukumar ta yi ga karfin kasar da mamaya da ta yi wa larduna uku na kasar Sham, kuma wannan na iya zama darasi a gare ku.

Har ila yau fitaccen farfesa a makarantar hauza na Najaf ya yi ishara da tsoma bakin da Amurka ke yi a kasar Iraki, inda ya bayyana cewa a kwanakin baya sojojin Amurka sun shiga filin jirgin saman Najaf ba tare da sanarwa da yarjewar jami'an tsaron Irakin ba, wanda hakan ke nufin mamaye kasar Iraki na hakika.

Ya jaddada cewa dole ne gwamnatin Iraki ta mai da hankali ga al'ummarta, ta kuma yi watsi da wannan mamaya a lokacin da jami'ai suka yi watsi da tsoma bakin Amurka, to jama'a za su mara masu baya. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi tsayin daka da mulkin mallaka na Amurka, don haka ne al'ummar Iran suka taru a kanta suka zama masu kare ta.

Ayatullah Musawi ya kammala hudubarsa da jaddada cewa har yanzu al'ummar Larabawa da na Musulunci suna da karfi da kuma iya fuskantar kalubale.

Your Comment

You are replying to: .
captcha