23 Nuwamba 2024 - 10:57
Gagarumin Hare-Haren Hezbollah Da Jirage Maras Matuki

A daidai lokacin da sojojin gwamnatin sahyoniyawan ke kokarin kutsawa ta kasa zuwa tsakiyar birnin Al-Khayam da ke da matukar muhimmanci a kudancin kasar Labanon, tashar Al-Manar ta bayar da labarin kaddamar da wani gagarumin hari da jiragen kunar bakin wake kan matattarar Sojojin Isra'ila a Al-Khaym.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa: Al-Manar dake da alaka da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kawo cewa, mayakan gwagwarmaya sun harba jirage marasa matuki guda 28 a wurin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka tattaru a birnin Al-Khaym da ke kudancin kasar Lebanon. Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai da jirage marasa matuka tun farkon arangamar yakin. Tun bayan da aka fara mataki na biyu na kai hare-hare ta kasa a kudancin kasar Labanon, gwamnatin yahudawan sahyoniya ta ke neman mamaye yankin mai tasiri na "Al Khayyam" wanda Isra’ila ke fuskantar tirjiya daga mayakan Hizbullah. Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a wannan yanki a daidai lokacin da ake kai hare-hare ta sama da na manyan bindigogin mamaya.

Hakanan kuma kamfanin labarai na Al-Arabi Al-Jadeed ya bayar da rahoton cewa a yau ranar Asabar aka gwabza fada tsakanin mayakan gwagwarmaya da sojojin gwamnatin sahyoniyawan a garin Al-Khayam da ke kudancin kasar Lebanon. Garin Al-Khayam yana da matukar muhimmanci a kudancin kasar Labanon yana cikin mawuyacin hali ta yadda Isra'ila ta lalata shi. Wannan gari, wanda ke da tarihi yana cike da yanayi mai tsanani ta hanyar da ya zamo hare-haren barna mai girma na Isra’ila ya same shi Isra'ila a kudancin Lebanon tsakanin shekarun 1982 zuwa 2000 da yakin Yuli 2006. A halin yanzu dai gidajensa da gine-ginensa na fuskantar tashin bama-bamai da rugujewa daga dakarun da suke mamaye. A sa'i daya kuma, ana kai hare-hare ta sama sosai, sannan kuma sojojin mamaya na ci gaba da kai masa hari da harsasan da kasashen duniya suka haramta amfani da su.

Wannan Garin Al-Khayyam wanda wani bangare ne da ke karkashin yankin "Marjayoun" a lardin Nabatie na kasar Labanon, yana da tazarar kilomita 5 daga shudin layin (layin da aka zana Majalisar Dinkin Duniya) tsakanin kasar Labanon da yankunan da aka mamaye kuma yana daya daga cikin garuruwa uku da sojojin mamaya ke kokarin kwacewa tun kwanaki 10 da suka gabata saboda muhimman dabarun yaki da suke da shi. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Labanon ya ruwaito; Sojojin mamaya sun yi ta kai hare-hare da bama-bamai da barna a wannan gari ta yadda za a ji karar fashewar abubuwa a garuruwan da ke kusa. Maharan sun shirya wannan aikin na rusau ne a daidai lokacin da ake kai hare-hare ta sama da na bindigogi.

shafin Al-Arabi Al-Jadeed ya rubuta cewa: A gefe guda kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana ci gaba da fuskantar sojojin mamaya a kudancin kasar Lebanon, musamman garin Al-Khayam, tare da kai wa cibiyar da suke hari da jirage marasa matuka Makamai masi linzami. Cibiyoyi takwas na tattaruwar sojojin Isra'ila a gabashi da kudancin matsugunin al-Khayam sun fuskanci hare-haren Hizbullah. Har ila yau, kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hari kan tankunan yaki na Merkava 2 a kudancin cibiyar tsare mutane ta Al-Khayam tare da lalata su. Cibiyar tsare mutanen ta Al-Khayam ita ce wurin da sojojin mamaya ke amfani da su a lokacin da suke mamaye kudancin Lebanon tsakanin 1982 zuwa 2000. An daure 'yan kasar Lebanon da yawa a gidan yari da azabtarwa a wannan wuri. Wannan wurin da ake tsare da shi ya zama alamar wahala da tashin hankali ta yadda fursunonin sun fuskanci gallazawa mafi muni. kuma bayan janyewar sojojin mamaya a cikin shekarar 2000 ya zama shaida game da laifukan mamaya.

A cewar wannan kafa, wannan karuwar hare-haren na Hizbullah na faruwa ne bayan da sojojin mamaya suka kaddamar da farmakin kasa na biyu a ranar 12 ga watan Nuwamba domin kutsawa cikin kudancin kasar Lebanon kuma a wannan rana ce kungiyar Hizbullah ta sanar da shirinta na yaki na dogon lokaci. Tun farkon mataki na biyu na harin kasa da aka kai a kudancin Lebanon, sojojin mamaya sun mayar da hankali kan fagage guda uku; Al-Khayyam a kudu maso gabas, Bint Jubeil a kudu da kuma garin "Shama" a kudu maso yamma. Sarrafa birnin Al-Khayam mai nisan mita 950 a saman teku, yana nufin iko da gabacin kudancin Lebanon har zuwa dajin garin "Hula" da yanke hanyar zuwa yankin Beka, wanda gwamnatin Isra'ila tana la'akari da wanna yanki a matsayin muhimmin sashi mai bayar da taimako ga Hizbullah.