Kamfanin dillancin labaran Abna:
Jagoran juyin juya halin Musulunci; A halin yanzu a cikin hudubar sallar juma'a yayi ishara da cewa: Manufa kur'ani ita ce hadin kan al'ummar musulmi, ma'ana Yana nufin cewa idan ku Musulmi kuka kasance da haɗin kai da tausaya wa juna, rahamar Allah za ta lullubeku a halin da kuke ciki.
Sannan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yayin hudubar juma'a ta yau: Ina yiwa dukkan 'yan uwana maza da mata da masoya da ni kaina wasiya da tsoron Allah a cikin maganganunmu da ayyukanmu, mu kiyaye kada mu wuce iyakokin Allah, ma'anar takawa kenan.
Yaci gaba da cewa: A cikin ayar da na karanta an tabo muhimmin batu na hadin kan muminai.
A cikin Alqur'ani an kira wannan alaqar hadin kan da wilaya.
Kuma A cikin wannan aya an baci cewa sakamakon wannan wiliyar da hadin a matsayin rahamar Ubangiji
Wato idan ku Musulmi kuka kasance da hadin kai da tausaya wa juna, rahamar Allah za ta baibayeku.
Karshen wannan ayar ya kare da ambaton darajar Ubangiji da hikimar Ubangiji.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin hudubarsa ta Juma'a ya ambaci cewa: makiyan al'ummar Iran sune dai makiyan al'ummar Palastinu, Labanon, Masar, Iraki da Yemen.
Kuma Manufar makiya ta bambanta, amma suna karbar umarni daga wuri guda.
Yakamata kowace al'umma ta bude idanunta tun daga farko idan har tana son kada ta sha wahala daga kawanyar makiya.
Ayatullah Khamenei: Makiya Iran da Lebanon da Palastinu da Iraki da Masar da Siriya da Yemen kwara daya ne.
Dole ne mu do
daura damarar kariya da tsaro tun daga Afghanistan zuwa Yemen, daga Iran zuwa Falasdinu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci; A yanzu haka a cikin hudubobin sallar Juma'a: makiyan Iran makiyan Palastinu ne da Labanon da Iraki da Masar da Siriya da Yemen.
Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da cewa Dole ne mu tsaurara ginshikin 'yancin kai daga Iran zuwa Gaza da Labanon da dukkan kasashen musulmi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa kowace al'umma tana da hakkin kare kasarta da yankinta daga wanda ya zalunce ta. Inda Jagoran juyin juya halin Musulunci yace Falasdinu na kare kasarta ne kuma guguwar Al-Aqsa ta halaltaciya ce Kariyar da Hizbullah ta ke yi wa Falasdinu da kuma aikin hare-haren tabbatttun alkawura guda su ma halastattau ne.
Jamhuriyar Musulunci tana yin aikinta ne da azama da azanci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci yaci gaba da cewa: guguwar Al-Aqsa wani yunkuri ne na shari'a daya halasta na kasa da kasa kuma Palasdinawa sune masu gaskiya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Gagarumin aikin harin da sojojin mu suka yi dare biyu ko uku da suka gabata aiki ne na shari'a kuma halastacce.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da cewa: Ba ma jinkiri ko gaggawar gudanar da ayyukanmu.
Zamu kawo maku cikakken fassarar matanin Hudubar nan gaba...