Innalillah WaInna Ilaihi Rajiuun
Hizbullah Ta Tabbatar Da Shahadar Sayyid Hasan Nasrullah Hizbullah Ta Tabbatar Da Shahadar Sayyid Hasan Nasrullah
Kungiyar Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Sayyid Hasan Nasrallah A Hukumance
Innalillah WaInna Ilaihi Raji'un
Sanarwar da kungiyar Hizbullah ta fitar bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah tazo kamar haka:
Kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa:
Da sunan Allah, Mai rahama Mai Jinkai.
"To, wadanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira, suka yi yaki a kan tafarkin Allah, wanda duk ya yi yaki a kan hanyar Allah, aka kashe shi ko ya yi nasara, za mu ba shi lada mai girma".
Sayyid shugaban gwagwarmaya, Bawa nagari, a matsayinsa na babban shahidi, jajirtaccen shugaba, jajirtacce, mai hikima, mai hangen nesa mumini, ya koma zuwa ga bakuncin da yardar Ubangijinsa, ya shiga cikin ayarin ma dawwama na shahidai. Mai hasken Karbala a cikin tafiyar imani ta Ubangiji bisa tafarkin annabawa da imamai shahidai.
Sayyid Hasan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bi sahun manya-manyan shahidansa madauwama wadanda suke kan tafarkinsu na tsawon shekaru kusan talatin, kuma a wannan lokaci ya jagoranci su daga nasara zuwa ga nasara sannan ya zama magajin Shugaban shahidan gwagwarmayar Musulunci a shekara ta 1371. Tun 'Yancin kasar Labanon a shekara ta 2000 har zuwa lokacin da aka Allah ya samar da nasara na dindindin a shekara ta 2006 da sauran yaƙe yaƙe na girmamawa da da daukar fansa har zuwa yakin goyon baya da jarumtaka na goyon bayan Palastinu da Gaza da kuma al'ummar Palastinu da ake zalunta.
Muna mika ta'aziyyarmu ga ma'abocin zamani (Allah ya kara masa yarda), da shugaba majibincin musulmi Sayyid Ali Khamene'i (Mudda zilluhul-Aali), da manyan maraja'ai, mujahidai da muminai har zuwa ga al'ummar gwagwarmaya, al'ummar mu masu juriya da mujahidai, da daukacin al'ummar musulmi, da dukkan 'yantattun duniya da ake zalunta da iyalansu masu daraja da hakuri, muna taya Sayyid Hasan Nasrallah Ridwan, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Ta'aziyya. Allah Ta'ala Ya jikansa a matsayin shahidin tafarkin Baitul Al-Maqdis da Palastinu. Ya zartar da umarnin Imam Husaini (as) ta hanyar harin ha'incin da yahudawan sahyoniya suka kai a yankunan kudancin kasar.
Jagorancin Hizbullah ya kai matakin maɗaukaki, mafi tsarki kuma mafi daraja a cikin tafiyar sadaukarwa da shahada da cewa, za mu ci gaba da jihadinmu da makiya, da tallafa wa Gaza da Palastinu, da kuma kare ƙasar Labanon mai ƙarfi da daraja
Kuma ga mujahidai masu daukaka da jajirtattun mayaka na gwagwarmayar Musulunci ku ne amanar shahidan masoyi kuma ku ne 'yan uwansa wadanda suka kasance garkuwarsa da ba za a iya cin nasara akanku ba kuma kambin jarumtaka da ceto shugabanmu da tunani mai tsarki da ruhinsa da tafarkinsa har yanzu yana tsakaninmu kuma zaku tabbata cikin alƙawarin aminci da riko da gwagwarmaya da sadaukarwa har zuwa nasara.
Asabar 7/7/1403
9/28/2024
24 Rabiul Awwal 1446 H