11 Oktoba 2025 - 14:40
Source: ABNA24
Iran: Hare-Haren Da Ake Kai Wa Tankunan Mai Na Iran Ba Za Su Tafi Ba A Banza Ba

Boroujerdi ya kara da cewa, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta AEO ya yi karin haske a wajen wannan taro kan yadda ake amfani da ilimin nukiliya a fagage daban-daban, inda ya yi nuni da nasarorin da aka samu a cikin gida a fannin noma da magunguna, musamman wajen magance raunukan masu fama da ciwon suga. Ya bayyana cewa wannan fasaha za ta iya ceto rayukan dubban mutane.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Aleddin Boroujerdi mamba a kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje na majalisar shawarar musulunci ya yi tsokaci kan wasu rahotanni dangane da yadda Amurka ke neman musgunawa jiragen ruwan dakon man fetur na kasar Iran, yana mai cewa irin karfin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi a cikin teku sananne ne ga Amurkawa, kuma sun taba gauraya da wannan karfin.

Ya kuma jaddada cewa, “Idan Amurkawa na son kawo wa tankokin mu matsala, to su sani cewa wannan hanyar da suka zaba tana da fuskoki biyu kuma ba za’ai shiru ga hakan ba.

Wakilin kwamitin tsaron kasa na majalisar ya kuma yi jawabi a taron da kwamitin ya yi a baya bayan nan da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, inda ya ce taron ya jaddada bukatar aiwatar da cikakken dokar da majalisar dokokin kasar ta zartar na dakatar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.

Boroujerdi ya kara da cewa, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta AEO ya yi karin haske a wajen wannan taro kan yadda ake amfani da ilimin nukiliya a fagage daban-daban, inda ya yi nuni da nasarorin da aka samu a cikin gida a fannin noma da magunguna, musamman wajen magance raunukan masu fama da ciwon suga. Ya bayyana cewa wannan fasaha za ta iya ceto rayukan dubban mutane.

Boroujerdi ya yi ishara da cewa, a cewar jami'an AEO, an samar da sabbin hanyoyin jiyya da suka dogara da fasahar nukiliya a kasar zuwa yau wadanda za su iya hana yanke gaba ga masu ciwon sukari. Ya bayyana cewa kawo yanzu wadannan hanyoyin sun ceci rayukan marasa lafiya kusan 2,000.

Boroujerdi ya jaddada yanayin zaman lafiya na ayyukan nukiliya na Iran yana mai cewa: Sabanin karyar sahyoniyawa da Amurkawa, Iran ba ta taba neman kera makaman kare dangi ba, kuma ba za ta taba neman yin hakan ba, wannan ilimi dai ana amfani da shi ne kawai don ci gaban kimiyya, masana'antu, da likitancin kasar.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha