23 Satumba 2024 - 18:13
Jiragen Yakin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Sake Kai Hare-Hare A Yankin Dahiya Birnin Beirut

Jiragen Yakin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Sake Kai Hare-Hare A Yankin Dahiya Birnin Beirut / Isra'ilawan Sun Yi Ikirarin Kashe Wani Jami'in Kungiyar Hizbullah.

An sake kai hare-hare ta sama a babban birnin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton cewa, an kai wasu hare-hare ta sama a yankunan kudancin birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.

A cewar wannan rahoto, jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan sun kai hari a yankunan kudancin birnin Beirut da makamai masu linzami 6.

Kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya sun yi ikirarin cewa, wanda aka nufa da wannan harin ta'addanci shi ne Ali Karki, wanda ya maye gurbin Fuw’ad Shukri kuma daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Hizbullah.

Har yanzu kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ba ta tabbatar ko musanta wannan labarin da aka buga ba.

Ya kamata a lura da cewa adadin shahidan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan kasar Labanon ya kai shahidai 274 wanda suka hada da kananan yara 21, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 1024. Sakamakon wadannan hare-hare, an tilastawa dubban mazauna yankuna daban-daban na Lebanon barin gidajensu.