19 Satumba 2024 - 19:48
Janar Salami: Nan Ba Da Dadews Ba Za Mu Ga Rugujewar Gwamnatin Sahyoniyawa Tare Da Mayar Da Martanin Ɓangaren Gwagwarmaya

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci a cikin wani sako da ya aike wa babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce: Makiya yahudawa sahyoniya ba za su isa ko'ina ba ta hanyar sabbin hare-haren ta'addanci da suke kai wa mata da maza da kananan yara na kasar Labanon.

A cikin shekara guda da ta gabata mayakan gwagwarmaya sun girgiza tushen tsaro na sahyoniyawan a cikin yankunan da aka mamaye, kuma makiya wadanda ba su iya fuskantar gaba da gaba suna aikata laifuka a baya don jinkirta mutuwarsu.

Duk da irin goyon bayan da yahudawan sahyuniya suke samu a yakin Gaza daga ƙasashen yamma ba su cimma ko daya daga cikin manufofinsu ba, kuma nan ba da jimawa ba za mu shaida yadda za a ruguza gwamnatin sahyoniyawan tare da martani mai murkushewa na gwagwarmayar.

Sardar Salami: Nan ba da dadewa ba gwamnatin sahyoniyawan za su dandana kudar ramuwar gayya da martanin yan gwagwarmaya, kuma za mu tunkari su.

Ba da daɗewa ba za a halakar da wannan halitta mai kisa.

Muna ba da wannan albishir ga jama'a da kuma dakarun gwagwarmaya, cewa akwai jerin hare-hare a nan gaba.