Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku bisa
nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Irna cewa: ma'aikatar lafiya ta kasar
Falasdinu ta sanar da cewa: A cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin
sahyoniyawan ta yi kisan kiyashi a zirin Gaza har sau 3, wanda a sakamakon
hakan mutane 55 ne suka yi shahada tare da wasu 110 na daban da su ka jikkata.
Bisa ga wannan rahoto da suka hada da wadannan shahidai, adadin shahidan a Gaza ya kai mutane dubu 39145, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai dubu 90257 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, a daidai lokacin da aka fara Dufanul Al-Aqsa.