6 Yuli 2024 - 13:25
Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Dangane Da Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Karo Na 14

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Sayyid Imam Ayatullah Sayyid Ali Khamenei Dama Zillhul Aali a cikin sakon godiya da girmamawa ga dukkan 'yan takara da masu fafutuka a fagen zabe, ya jaddada bukatar amfani da dimbin karfin da zababben shugaban kasar ke da shi wajen jin dadin al'ummar kasar da ci gaban kasar, tare da ci gaba da bin tafarkin Shahid Shugaba Ibrahim Raisi.

Nassin Sakon Nasa Shi Ne Kamar Haka:

 Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

بسم الله الرّحمن الرّحیم

والحمد لله ربّ العالمین والصلاة والسلام علی سیدنا محمدٍ و آله الطاهرین سیما بقیّة الله روحی فداه.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Sayyidina Muhammad da alayensa tsarkaka musamman Bakiyyatulh rai na fansa gare shi.

Godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mai jin kai, kasancewar da yardarsa da nasararsa, al'ummar Iran mai girma bayan mummunan musibar rashin shahid shugaban kasar ta samu damar shirya fage na zaben shugaban kasa cikin kankanin lokaci na shari'a tare da gudanar da zabuka cikin gaskiya da adalci a ranakun Juma'a biyu a jere, inda ta zabi shugaban kasar daga cikin 'yan takara suka samu rinjayen kuri'u.

Jami'an zabuka masu girma sun gudanar da ayyukansu cikin gaggawa da cikakkiyar amana, sannan kuma al’umma masu daraja sun fito fagen tare da jin nauyin da ya hau kansu, suka samar da yanayi mai dadi da kishi tare da tara takardun zaben a matakai biyu da sama da miliyan 55 na kuri'u.

Wannan gagarumin yunkuri na tunkarar hayaniyar a kauracewa zabe, wanda makiya al'ummar Iran suka kaddamar da ita don haifar da yanke kauna da tashe-tashen hankula, - hakan da su ka yi- aiki ne mai kayatarwa da ba za a manta da shi ba, da dukkanin 'yan takara masu daraja da dukkan wadanda suka yi aiki dare da rana tsawon makonni don nasarar kowannensu suna rabon daraja da lada.

Yanzu dai al'ummar Iran sun zabi shugabansu. Ina taya al’ummar kasa da zababben shugaban kasa da daukacin masu fafutuka na wannan fage mai matukar muhimmanci, musamman ma matasa masu kishin bangarorin ‘yan takara, ina ba da shawarar kowa da kowa ya ba da hadin kai da tunani mai kyau don ci gaba da kara daukakar kasar nan. Ya dace a canza dabi’un gasa a lokacin zabe zuwa dabi’un abokantaka kuma kowa ya yi iya kokarinsa don raya bangarorin jiki da ruhiyyar kasa.

Ina kuma ba da shawara ga zababben shugaban kasa Dr. Pizishkian, da ya dogara ga Allah Mai Rahama ya yi dogon dubi ga tsororuwar hadafi mai haske, bisa ci gaba da tafarkin Shahidi Raisi, ya yi amfani da damarmaki ayyukan kasar nan musamman ayyukan matasa, masu neman sauyi da masu rike da madafun iko, don jin dadin jama’a da ci gaban kasa.

Na sake mika godiya da na kuma girmama tunawa da shahidai masu girma da kuma babban limamin shahidai, da kuma dukkan ’yan takara masu daraja da masu fafutuka a fagen zabe da suka taka rawa a wannan mawuyacin lokaci, da kuma kafafen yada labarai ina mika godiyata ga jami’an tsaron kasa da jami’an tabbatar da zabe.

Sayyid Ali Khamenei / 4/16/1403