20 Yuni 2024 - 14:37
Me Ya Faru A Hajjin Bankwana Da Gadir Khum Mutane Sama Da Dubu 100 Ne Suka Halacci Hajjin

Manzon Allah (SAWA): “Ku Saurara Wanda! Yake Nan Ya Sanarwa Wanda Baya Nan”. Da Fadarsa (SAWA: "Allah Yayi Albarka Ga Mutumin Da Yaji Maganata Ya Riketa Kuma Ya Fadeta Zuwa Ga Wanda Bai Ji Ta Ba. Idan muka kiyasta adadin sahhaban da suka ruwaito hadisin Gadir wanda suka kasance kusan sahabbai 120 da adadin wadanda suka halarta tare da shidawa da ji da gani zasu zamo daya kaso daya ne bisa dubu to kaga kena maruwaita hadisin yan kadan ne matuka

بسم الله الرحمن الرحيم

الحمد لله العلي القدير العليم الخبير، السميع البصير، والصلاة والسلام على البشير النذير، السراج المنير، وعلى آله المنزّهين عن الرجس بنصّ آية التطهير، ولا سيّما سيّد الوصيين وأمير المؤمنين المنصوب بيوم الغدير، ولعنة الله على أعدائهم أصحاب السعير.

Hakika ya kasance a hajjin bankwana da manzon Alllah (SAWA) ya yi a shekara ta goma bayan hijra, a kan hanyar komawarsa daga Makka zuwa Madina a wani guri da ake cewa Juhfa a wajen wani kawarin ruwa da ake cwa Gadir Khum wanda waki’ar Gadir ta faru a ranar 18 g watan Zulhijjah a shekara ta 10 bayan hijirar Annabin Rahama daga Makka Zuwa Madina.

Hadisin Waki’ar Gadie Khum hadisi ne da aka rubuta daruruwan littafai a suka kai sama da littafi  162 daga wanda suke kunshe da riwayoyin manyan sahabbai da tabia’ai wanda hadisin ya kai haddin matsayin tawaturi da ba za’a iya karyata shi ba. Wanda sahabbai kusan 120 ne suka ruwaici hadisin, wanda ba zaka samu yawan adadin masu ruwaioto hadisi kamar haka a wasu sauran hadisai da aka ruwaito ba. Kai koma rabin adadin masu wannan ruwayar a wani hadisin ba zak samu ba, domin maruwaita wannan hadisin suna da yawa matuka.

Idan muka dubi lamari ta wata fuskar zamu ga Annabin Rahama bai fadi wannan hadisin a tsakar gidansa ko a cikin masallacinsa ko a cikin wasu gungu kadan na sahabbansa ba, sai dai ya bayyana fadinsa yana mai shewa a cikin taron mutane da birnin madina bai ishe su, ya fadi hakan aciin taron mutane d asuke cikin falalin sahara mai fadi a mafi girman taro na musulunci da tarihi ya shaida a zamanin manzon Rahama (SAWA).

Ibn Sa’ad a cikin littafinsa Dabaqat juzu’i na biyu shafi na 171 ya ce: sai manzo Allah ya yayi niyyar fita zuwa aikin Hajji kuma ya shelantawa mutane da hakan, sai mutane masu yawa suka zo Madina domin suyi koyi da manzon Allah (SAWA) a hajjinsa...

Shima Ibn Hibban ya anbaci irin wannan maganar ta ibn Sa’ad a juzi’i na biyu na littafin Siqat shafi na 124.

Wanda wannan riwayar an curo ta daga hadisin Jabir wanda Imam Muslim ya kawo a cikin littafin Sahihinsa juzu’i na biyu shafi na 886 nambar hadisi ta 1218 babin hajjin Annabi (SAWA) in ya ce: Lalle manzon Allah (SAWA) ya zauna a Madina shekara tara sannan ya shelantawa mutane -yin hajji- a shekara ta goma  da cewa: Lalle Manzon Allah (SAWA) yana da nufin fita hajji, sai mutane daywa suka shigo Madina dukkansu suna so ya zama sun koyi da Manzon Allah (SAWA) kuma sun yi aikata irin aikin daya aikata sai mutane suka fita tare da shi –Manzon Allah (SAWA)- har sai da suka zo Zul Hulaifa... sai Manzon Allah (SAWA) yayi sallah a masallaci sanna ya hau tgauwarsa Quswa’u, har sai da taguwarsa ta daidaita da tafiya a akan sahara sai na duba iya ganina a gabansa da damarsa da hagunsa da bayansa ba wanda nake gani sai mahayi ko matafiya da kafa kawai...

Shi ma Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Almusannaf ya kawo cewa: sai jabir ya ce: sai mutane dayawa suka shigo Madina dukkansu suna son suyi koyi da manzon Allah (SAWA) kuma suyi aikata irin abunda ya ya aikata. A cikin littafin Musnadil Himyari 1288 daga jabir ya ce; An yi shelar hajji da cewa lalle manzon Allah (SAWA ya nason yin hajji sai Madina ta cika. -da mutane-.

A wani hadisin kuma na Jabir wanda Abu Ya’ala a Musnadinsa ya fitar da shi sau biyu a juzu’i na hudu shafi na 24 namba ta 2027 da kuma a juzu’i na sha biyu shafi na 106 namba ta 6739 Jabir ya ce: sai na duba gabana da bayana da damata da haguna iayakar ganina mutane ne kawai masu tafiya a kafa da masu tafe akan abun hawa...

Shima Ibn Shair ya fada a juzu’i na farko na littafin Uyunut Tarik shafi na 394 cewa: kuma Sahabbai dubu 100 ne dama sama da haka su kai Hajji tare da Manzon Allah (SWA) har sai da ya zamo wand bai taba ganin manzo ba kafinta ko bayanta sun yi hajji tare da shi kuma sun sabmu matsayin Sahabbanci da ita...

Sannan Sibd Ibnul Jauzi ya fada a cikin littfainsa Tazkiratu Khawasul Ummah acikin maganar dagane da hadisin Gadir Khum a shafi na 30:” ya kasance a tare da Manzon Allah (SAWA) akwai sahabbai da kuma larabawan kauye wadanda ssuke zaune a Makka da Madina da sukai kai mutum dubu 120 sune wadanda suka halarci hajji tare da shi kuma suka ji wanna zancen daga gares shi...”.

Idan muka kiyasata adadin sahhaban da suka ruwaito hadisin Gadir wanda suka kasance kusan sahabbai 120 da adadin wadanda suka halarta tare da shidawa da ji da gani zasu zamo daya kaso daya ne bisa dubu to kaga kena maruwaita hadisin yan kadan ne matuka.

Duk da cewa Manzon Allah (SAWA) ya tabbatar masu ba waje daya ba, da kuma a wannan wajen nasa inda yace: “Ku Saurara Wanda! Yake Nan Ya Sanarwa Wanda Baya Nan”. Da kuma fadarsa (SAWA: Allah yayi albarka ga mutumin da yaji maganata ya ya riketa kuma ya fadeta zuwa ga wanda bai ji ta ba.

Ko da ace bai fadi hakan a wannan wajen ba, hakika ya fadi haka a hudubarsa da yayi a Haifa daga Mina kuma hakan bai wuce yan kwanaki ba.

Amma sai dai yayin da Manzon Allah (SAWA yayi wafati kuma ba’a zartar da abunda yake so ba, sai mutane suka yi akan ruwaito wanna hadisin kuma suka yi shiru akan ruwaito hadisai masu kama da wannan. Kai harma aka hana ruwaito falaloli da matsayi na Amirul Mu’uminina Ali As kuma aka hana mutane a bayyane kan ruwaito hadisi daga Manzon Allah (SAWA.

Kai har ta kai ga an umarci mutane su rika zagin Amiril Mu’uminina Ali As kuma aka koya masu zaginsa, duk da Imam Ali As ya basu labarin hakan kafin faruwarsa da cewa: “ ku saurara tabbas za’a bijro maku da zagina da barranata daga gareni amma in ance ku zagen ku zageni....

Hakan  yasa mutane suka mance haidisin Gadir da kuma nassin da yayi nuni akan Khalifancinsa kai ba ma haka har ma suka mance daukaka da matsayin Imam Ali As.

Za Mu CI Gaba Insha Allah....