17 Agusta 2023 - 10:17
Iran: Amir Abdullahian Ya Tafi Riyadh

Hussein Amirabdollahian, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a matsayin shugaban wata tawaga da kuma amsa gayyatar da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya yi masa, ya bar Tehran zuwa Riyadh.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin wannan tafiya za a tattauna da musanyar batutuwa daban-daban da suka shafi alakar kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu a fagen duniyar Musulunci, shiyya-shiyya da na kasa da kasa.